- Marubuci, Paul Melly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa analyst
A wata alama ta ci gaban taɓarɓarewar dangantaka, sojojin da ke mulki a Nijar sun nuna ƙarara a shirye suke wajen korar Faransa daga kowane ɓangare na tattalin arzikin ƙasar – musamman ma haƙar uranium.
A wannan mako ne kamfanin makamashin nukiliya na Faransa Orano, ya ce gwamnatin soji ta Nijar da ta hamɓarar da shugaba Mohamed Bazoum a watan Yunin 2023, ta ƙwace ayyukan da ake yi na haƙo Uranium a ƙasar.
Ƙoƙarin da kamfanin ya yi na komawa fitar da makamashin uranium ya gamu da cikas daga sojojin da ke mulki na tsawon watanni, kuma hakan ya jefa ta cikin matsalar kuɗi.
Kuma za a ji tasirin haka a faɗin ƙasar – duk da cewa Nijar na samar da ƙasa da kashi biyar na uranium da ake samarwa a duniya, a 2022 ta samar da rabin uranium da aka fitar zuwa faɗin Turai.
Saboda haka lamarin zai jawo wahala, yayin da ƙasashen yamma ke fafutukar magance matsalar sauyin yanayi da kuma rage gurɓataccen iska da ke fita daga wutar lantarki.
Ga shugaba Emmanuel Macron, wanda a halin yanzu yake fama da matsin siyasa a gida, ficewar kamfanin Orano daga Nijar zai zama babban kalubale.
Saboda hakan ya zo daidai da labaran da suka daɗe suna fitowa daga ƙasashen Afrika – Chadi ma ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da Faransa, yayin da Senegal ta ce za ta rufe sansanin sojin Faransa da ke Dakar.
Amma a kowane hali, rikicin da ke fuskantar Orano a Nijar yana a matsayin babban kalubale ga Faransa wajen samun makamashin.
Ƙasa mai tashoshin nukiliya 18, waɗanda ke samar da kusan kashi 65 na wutar lantarki, Faransa ta kasance a gaba wajen fitar da gurɓataccen hayaki daga ɓangaren wutar lantarki.
Amma ƙarancin sinadarin Uranium da ƙasar ke samarwa ya kawo karshe fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Don haka, a cikin shekaru goma da suka wuce, ta shigo da kusan tan 90,000 – kashi biyar na hakan daga Nijar. Kazakhstan – wadda ke da kashi 45 na abubuwan da ake fitarwa a duniya – ta kasance wuri mafi muhimmanci.
Ci gaba ko kuma dakatar da ayyukan kamfanin Orano a Nijar, zai janyo Faransa ta juya zuwa wasu wurare.
Za ta iya komawa wasu wurare domin samun makamashin, ƙasashe irin su Uzbekistan da Australia da kuma Namibia.
A bara, yayin da ƙasashen Afrika ta yamma makwabtan Nijar suka saka mata takunkumin kasuwanci da ya janyo matsala wajen fitar da uranium, wasu sun yi amfani da damar wajen samun makamashin.
Ma’adinan da Tarayyar Turai ke shiga da su daga ƙasar ya ragu da kashi uku, amma Canada ta maye gurbinsu.
Amma akwai alamu da ke nuna cewa akwai batun siyasa a ciki. Makamashin uranium da Tarayyar Turai ke shigo da su daga Rasha ya karu da fiye da kashi 70, duk da tsauraran takunkumin da aka kakaba wa Moscow saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.
Kuma tabbas, Rasha ta zama sabuwar babbar ƙawar shugabannin sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar da makwabtanta, Burkina Faso da Mali, tun daga shekarar 2020.
Sojojin Rasha sun yi aiki tare da sojojin Mali a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi da ‘yan kabilar Tuareg, yayin da kuma suke taimakawa wajen kare manyan jami’an gwamnatin mulkin soja a Nijar da Burkina Faso.
Don haka, ko da yake Faransa da Turai, za su iya nemo hanyoyin da za a bi don tinƙarar rashin ma’adinin uranium daga Nijar, sauyin ba zai yi daɗi ba.
A cikin ɗan ƙankanin lokaci, ƙasashen Turai za su ƙara dogaro da Rasha da maƙwabtanta na tsakiyar Asiya, ba tare da tunanin matsin tattalin arziƙi da hakan zai yi kan shugaba Vladimir Putin ba, a wani lokaci mai mahimmanci a rikicin Ukraine.
Bugu da kari, gwamnatin Nijar wadda dangantakar ta da Tarayyar Turai ta kusan lalacewa yayin da ta raba gari da Faransa, ƙasar na ci gaba da neman wasu hanyoyin da za ta bi wajen kulla ƙawancen da ƙasashen yamma.
Tana duba yiwuwar kulla alaƙar kasuwanci da Iran – musamman wajen fitar da uranium ɗin ta.
Tuntuɓar juna tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu na ƙara zurfafa, yayin da Firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya ziyarci Tehran a watan Janairu.
Jita-jita na yiwuwar kulla yarjejeniyar samar da uranium da Iran ɗin ta bazu a ƴan watanni da suka wuce.
A halin da ake ciki, burin Orano na komawa haƙa da fitar da uranium daga Nijar ya citura, idan aka yi la’akari da halin ba sani ba sabo na gwamnatin soja a Yamai.
Ko a lokacin da aka hamɓarar da Bazoum a watan Yulin 2023, shugaba Macron ya yi Alla-wadai da lamarin ganin cewa ya kasance ɗaya daga cikin abokansa na siyasa da tsaro a Afrika.
Paris ta amince da matsayar ƙungiyar Ecowas, har ma akwai jita-jitar cewa ta yiwu a shirye take ta ba da goyon baya idan ƙungiyar ta ɗauki matakin amfani da karfin soja a Nijar don mayar da Bazoum.
A cikin wannan yanayi na rashin daɗi da yarda, Orano ya kasance ramuwar gayya ga sojojin da ke mulki.
Rawar da kamfanin na Orano ya taka wajen haƙar uranium a Nijar, ya fusata ƴan ƙasar da dama a tsawon shekaru, a daidai lokacin da ake zargin cewa kamfanin na Faransa na sayen uranium cikin rahusa, duk da sake inganta yarjejeniyar fitar da shi waje.
Duk da cewa an fara aikin haƙar ma’adinai a ƙasar shekaru bayan samun ƴancin kai, ana ci gaba da kallonsa a matsayin tasirin da Faransa ke da shi bayan mulkin mallaka da ta yi wa ƙasar.
Bayan juyin mulkin bara, Orano ya yi ƙoƙarin kauce wa takun tsakar diflomasiyya da ta ɓarke, inda ya ci gaba da aikinsa yadda ya kamata.
Sai dai takunkumin da Ecowas ta kakaba wa Nijar ya hana kamfanin fitar da uranium daga wajen haƙar ma’adinai na Somaïr, kusa da Arlit, a yankin Sahara.
Kuma duk da ɗage takunkuman a karshen watan Febrairu, hanyar fitar da uranium ɗin ta wani ɓangare na ƙasar Benin, ya ci gaba da kasancewa a rufe saboda sojojin da ke mulki sun bar shi a kulle sakamakon saɓanin siyasa da Benin ɗin.
Orana ya buƙaci fitar da uranium ɗin waje, sai dai gwamnatin mulkin sojin ta yi watsi da hakan.
A watan Yuni, sojojin suka soke ƴancin da kamfanin na Faransa ke da shi na gina sabon wurin haƙar ma’adinai, wadda ake ganin zai ƙara bunƙasa ci gaban ɓangaren.
Lokacin da Orano ya yanke shawarar dakatar da haƙar ma’adinai da mayar da hankali kan biyan albashin ma’aikata, dangantaka da gwamnatin mulkin sojin ta ƙara taɓarɓarewa.
Ba kamfanin kaɗai ba, har ma tattalin arzikin Nijar zai ɗanɗana kuɗarsa kan wannan yanayi da aka shiga, ta hanyar rasa kuɗaɗen da yake samu a fitar da uranium da kuma rasa ɗaruruwan ayyuka.
Ga Arlit da sauran al’ummomi a yankin arewacin sahara, wannan babbar koma baya ne, duk da sake farfaɗo da batun haƙar ma’adinai na China a yankin da kuma yadda masu hulɗa ke nuna sha’awa ga ɓangaren.
Sai dai sojojin da ke mulki a Nijar ba su da buƙatar amincewa Orano saboda a yanzu hanakalinta ya koma kan ƙaruwar fitar da mai, sanadiyyar wani sabon bututu da China ta gina.
Dangane da haka, gwamnatin ƙasar ta shirya aiki ba tare da fitar da uranium da ta saba yi ba da Faransa – wadda a yanzu ta zama abokiyar adawarta ta waje.