Shugabannin ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka, Ecowas, sun yi wani taro a Abuja, babban birnin Najeriya, inda suka mayar da hankali a kan ficewar ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar daga ƙungiyar mai mambobi 15.
Yayin da ƙungiyar ke fafutukar haɗa kan yankin yammacin Afirka, tana shirin fara wani katafaren aikin hanya mai nisan kilomita 1,028 wanda ya tashi daga Abidjan, babban birnin Ivory Coast, ya ratsa ta Ghana, ya shiga Togo da Benin sannan ya ƙarasa Lagos, birni mafi girma a Najeriya.
An shirya cewa za a fara aikin hanyar a 2026, kuma tuni aka samu masu zuba jari da suka amince da zuba kuɗi dala biliyan 15.6 (£12.3bn) domin aiwatar da aikin.
Ecowas tana fatan samar da ayyukan ci gaban ƙasa ga jama’ar ƙasashe mambobinta a matsayin hanya ta shawo kan guguwar juyin mulki da yankin ke fuskanta tun daga 2020, kamar dai irin salon da yammacin Turai ta yi amfani da shi wajen kafa kanta a shekarun baya.
An fara tsara aikin samar da hanyar sufuri da za ta haɗa ƙasashen yammacin Afirka tun shekaru takwas da suka gabata, tun kafin juyin mulkin da ya kifar da gwamnatoci a Mali, Burkina Faso, da Nijar.
Bankin bunƙasa Afirka ne ya shige gaba wajen gabatar da rahoton nazarin da aka yi domin tabbatuwar aikin.
A yanzu ana iya cewa ƙungiyar Ecowas ta samu damar aiwatar da wannan aiki a daidai lokacin da take matuƙar buƙatar ayyuka irin shi, wanda za su farfaɗo da martabar ta da kuma dawo da kakkyawar fata tsakanin jama’ar yankin, game da ayyukan ƙungiyar.
Duk hanyoyin da Ecowas ta bi wajen tursasa wa sojojin Nijar domin su kafa gwamnatin farar hula sun gagara, kuma ƙungiyar ta bi hanyar lalama da barazanar amfani da ƙarfin soji da kuma ƙaƙaba wa ƙasar tukunkumi, amma duk haƙa ba ta cimma ruwa ba.
Ƙasashen uku sun haɗa kai wajen fitar da sanarwar ficewarsu daga cikin ƙungiyar Ecowas mai ƙasashen 15.
Da wannan sanarwa sun kawo cikas ga fatan sauran mambobin ƙungiyar ta ganin an shawo kansu, duk da cewa wakili na musamman da Ecowas ta naɗa domin shawo kan ƙasashen, kuma sabon shugaban ƙasar Senegal, wanda matashi ne, yana ci gaba da ƙoƙarin karkato da ƙasashen.
Kafin wannan dambarwa, Ecowas ce ƙungiya mafi ƙarfi da kafuwa a Afirka, inda take da ƙarfin faɗa a ji a fannin siyasa da kwantar da rikici, ta yadda har sojoji take turawa ƙasashe masu fama da rikici domin taimakawa wajen samar da zaman lafiya.
Da ficewar Mali, Burkina, da Nijar, ƙungiyar za ta yi asarar mutane miliyan 76 daga cikin miliyan 446 da take da su, kuma za ta yi asarar kusan rabin faɗin ƙasar da take da ita, wanda kuma koma baya ne gare ta.
An ƙirƙiro wannan katafaren aikin titi da zai haɗa ƙasashe domin bunƙasa harkokin tattalin arziki, amma zai iya zama wata hanya ta samun nasarar siyasa, inda zai yi nuni da ƙarfin da sauran ƙasashen ƙungiyar ke ta shi wajen haɗa kai da bunƙasa kasuwanci tsakanin su da kuma janyo masu zuba jari zuwa yankin da ya fi kowanne bunƙasar tattalin arziki a Afirka.
Kuma kamar yadda ƙarfin arziki da bunƙasar ƙungiyar tarayyar Turai ya janyo ƙasashen cikin ta, itama Ecowas za ta iya faɗaɗa mambobinta zuwa ƙasashen yankin arewacin Afirka.
An yi hasashen cewa aikin katafaren titin mai hannu huɗu zuwa shida zai samar da aikin yi ga mutum 70,000, kuma ana sa ran kammala shi a 2030.
Tsarin da aka yi shi ne samar da wadatacciyar hanya wadda nan gaba za a bi wajen shimfiɗa layin dogo da zai haɗa ƙasashen Ecowas.
Hanyar za ta haɗa manyan biranen yammacin Afirka da dama daga Abidjan mai mutane miliyan 8.3 zuwa Accra mai mutane miliyan 4, da Lome mai mutane miliyan 2, da Cotonou mai mutane miliyan 2.6 har zuwa Lagos mai mutane miliyan 20.
Da dama a cikin biranen dai sun zamo wata mashiga ta hada-hadar kasuwanci a ciki da wajen yankin.
Tuni dai aka fara bayyana damuwa a kan barazanar wanzuwar rashawa da dama can ana fama da ita a tsakanin jami’ai da direbobin da ke bin hanyoyin da ke tsakanin ƙasashen.
A kan iyakokin ƙasashen yankin ne za ka samu jami’an tsaro suna duba takardun tafiya na mutanen da za su wuce, inda direbobi da matafiya ke jan dogon layi domin a tantance su kafin shiga ko fita ƙasashen.
Haka nan kuma samar da wannan babbar hanya da kuma layin dogo zai ƙara bunƙasa hada-hadar ƙasuwanci da tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen da kuma kawo sauyi a fannin zuba jari, kamar dai yadda aka samar a ƙarƙashin ƙungiyar tarayyar Turai.
Kuma hanyar bunƙasa tattalin arziki da daidaiton shugabanci za ta kawo ci gaban siyasa da alaƙar ƙasashe.
Za ta kuma zama hanya mai ƙarfi da za a janyo hankalin ƙasashen da basu riga sun shiga ƙungiyar Ecowas ba, domin su ƙara bunkasa harkokin tattalin arzikin su, da samar da shugabanci nagari, da kuma yaƙi da rashawa saboda fatan samun damar shiga Ecowas.
Ecowas tana da damar amfani da wannan katafaren aiki wajen janyo hankalin ƙasashen da suka fice domin ganin sun ƙara komawa cikin ta, ta hanyar tallata irin alfanun da ke tattare da shimfiɗa hanyar, musamman a fannin bunƙasa tattalin arziki.
Ƙasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso duk suna fuskantar ƙalubalen ci gaba da kuma na tsaro, gashi kuma sun dogara ne ga maƙwabtansu masu madatsun ruwa a harkar jigilar kayyaki da kasuwanci.
Ana gudanar da hada-hadar kasuwanci mai yawan gaske a kan iyakokin ƙasashen Afirka ta Yamma, ko dai a hukumance ko kuma wanda ake yi ta bayan fage.
Ana jigilar dabbobi daga ƙasashen uku da suka fita daga Ecowas domin kai wa Dakar da Abidjan da kuma Lagos.
Daga Nijar, ana fitar da Albasa da Dankali zuwa Ivory Coast da kuma Ghana, yayin da ake jigilar kayan da aka yi a Najeriya zuwa Nijar da sauran ƙasashe.
Akwai miliyoyin ƴan Burkina Faso da Mali da ke zaune a Ivory Coast, inda suke hada-hadar kasuwanci da noma.
Bugu da ƙari, jagororin juyin mulki a yammacin Afirka ba su janye daga haɗakar samar da kuɗin bai ɗaya na CFA a yankin ba, wanda yunƙuri ne da Faransa ke goyon baya kuma ake yi wa kallon hanyar da za a magance hauhawar farashin kayayyaki.
Amma duk da waɗannan abubuwa, ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar ba su fasa sanar da ficewar su daga ƙungiyar Ecowas ba.
Turjiyar da ƙasashen suka yi wa Ecowas ta janyo masu ƙara farin jini a tsakanin jama’ar su, kuma yanzu haka Morocco ta yi masu tayin buɗe kafar faɗaɗa alaƙar kasuwanci da su.
Amma idan sauran ƙasashen Ecowas za su faɗaɗa damar da suke da ita ta kawo ayyukan ci gaba, musamman irin aikin gina hanyar motar da suke shirin yi, da samar da layin dogo, da janye shamakin kasuwanci a tsakaninsu da ƙasashen uku na yankin saharar sahel, za su iya dawo da su cikin ƙungiyar da haɗa kan yammacin Afirka baki ɗaya.