Majalisar dattijan Najeriya ta cire sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume daga muƙamin mai tsawatarwa.
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a yau Laraba bayan ƙorafi da jam’iyyar APC, mai mulki ta yi kan wasu kalaman sanatan a baya-bayan nan.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto wata wasiƙar ƙorafi daga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma sakatarenta, Sanata Bashir Ajibola.
Wasiƙar ta zargi Sanata Ndume da furta wasu kalamai waɗanda ke iya zubar da ƙimar gwamnati da kuma karya gwiwar masu son shigowa ƙasar domin zuba jari.
Bayan karanta wasiƙar ne Sanata Akpabio ya nemi a kaɗa ƙuri’a domin amincewa ko watsi da buƙatar kuma daga ƙarshe sanatocin suka zaɓi tsige Ndume.
Haka nan kuma majalisar ta cire Ndume daga muƙaminsa na mataimakin shugfaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar.
Majalisar ta ce a yanzu an mayar da sanatan zuwa kwamitin harkokin yawon shaƙatawa.
Nan take kuma aka zaɓi Sanata Tahir Munguno domin maye gurbin Sanata Ali Ndume.
Ali Ndume, sanata ne wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar manufofin gwamnati, yayin da magoya bayansa ke masa kallon mai faɗin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Majalisar Dattijan Najeriyar ta dakatar da wani wakili na ta ba.
Ko a watan Maris ɗin 2024 majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya daga majalisar bayan zargin sa da furta “kalamai da ke iya zubar da ƙimar majalisar.”
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan wata tattaunawa da sanatan ya yi da kafar yada labarai ta BBC, inda ya yi zargin cushe a cikin kasafin kudin ƙasar.