Muhawarar ciwo sabon bashi da Majalisar Dattawa ta amince da shi dai na kara kamari ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kan tsadar rayuwa suna mai cewa a ganin su ya kamata a ce cire tallafi man fetur da aka yi zai dakile zancen karbo sabbin basussuka daga kasashe masu karfin tattalin arziki.
A halin matsin da ake ciki dai musamman ma ganin sabon rancen dala biliyan 2 da digo 2 da Majalisar Dattawa ta amince da shi, masana da dama na cewa, dole ne a wayar da kan al’umma don takurawa gwamnati ta aiwatar da ababen da talakawa zasu sami saukin rayuwa.
A cikin makon Jiya ne Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu, na karbo rancen dala biliyan 2.2, domin aiwatar da wani bangare na gibin kasafin kudin shekarar 2024 na naira tiriliyan 9.7, amincewar da ta biyo bayan gabatar da rahoton da Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa akan basukan gida da na waje, Aliyu Wamakko, ya gabatar yayin zaman majalisar.
Tuni dai ‘yan Najeriya ke ci gaba da nuna rashin amincewarsu da wannan sabon rance inda wasu ke cewa ana yunkurin saryantar da ‘yancin kasar.
Adadin bashin da ke kan Najeriya wanda ya hada da na cikin gida da waje ya kai Naira Triliyan 134.30 kwatankwancin dalar Amurka biliyan 91.35 a cikin Zango na 2 na shekarar nan daga Naira triliyan 121. 67 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 91.46 da aka samu a zango na cQ1 2024.
Saurari cikakken rahoton: