A yayin bukin ranar tunawa da ‘yancin bil’adama, kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ci gaba da take hakkokin bil’adama a jihar Zamfara. Sun bayyana irin mawuyacin halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki, ciki har da rahotannin fyade da sauran nau’ikan tashe-tashen hankula.
Wadannan kungiyoyi sun jaddada cewa rashin tsaro ya zama babban shinge na farko da ke kawo cikas ga sha’anin ci gaba a Zamfara, wanda ke kara ta’azzara talauci da take hakkin bil’adama.
Ahmad Hashim, shine jami’an Kula da shirye shirye na waya Kungiyar Kula da yan gudun hijira, yace “ana take hakkin yan gudun hijira ta hanyar hana su samun Abinci da muhalli da kiwon lafiya da dai Sauran su.”
Ita kuwa Zaunab Nuhu ta kungiyar Kare hakkin mata cewa tayi “rashin tsaro a jihar na cigaba da jefa yan gudun hijira cikin mawuyacin hali musamman na cin zarafi da muzguna masu a wannan gari.”
An jaddada batutuwan da suka fi daukar hankali a jihar a yayin bikin ranar kare hakkin bil’adama ta duniya, inda masu fafutuka da masu aikin jinkai suka yi kira da a dauki matakin gaggawa don magance tauye hakkin bil’adama da ke kara ta’azzara a yankin. Da yawa sun yi nuni da cewa rashin samun sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar ya sa ‘yan gudun hijirar fuskantar matsaloli.
A nashi haujin, Shugaban hukumar Kare hakkin biladama ta Kasa reshen jihar Zamfara, Abdullahi Abubakar yace akwai bukatar masu Ruwa da tsaki su tashi tsaye don magance matsalar.
“Abun kullum kara yawa yakeyi, muna yawan samun korafe korafe akan take hakkin biladama, gaskiya ya dace gwamnati ta dauki wani mataki.”
A wani yunkuri na rage radadin talauci da rashin tsaro, gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya kaddamar da shirin mika kudi. Shirin yana nufin tallafa wa al’ummomi masu rauni. Mutane dubu arba’in da hudu (44,000) za su amfana, ciki har da matasa, masu bukatu na musamman, da kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa. Ana kallon shirin a matsayin wani kyakkyawan mataki na dakile kalubalen tattalin arziki da kalubalen tsaro ya haddasa a Jihar.
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, kalubalen tsaron da jihar fama da shi yayi sauki kuma suna nan suna aiki tukuru don ganin an samu kwanciyar hankali.
“Idan na ce ma babu yan gudun hijira banyi adalchi ba, amma mun samarda wani kwamiti da zai yi aikin tantance su don gano yawan su dakuma yadda za mu taimake su da Abinci da Magani da muhalli da dai sauran su “ Inji Gwamna Dauda Lawal
Duk da haka, ma’aikatan jinkai sun lura cewa, duk da cewa irin wadannan shirye-shiryen suna da mahimmanci, ba su isa su magance cikakken yanayin rikicin ba. Yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu na ci gaba da fama da yanayin rayuwa na tashe-tashen hankula da kauracewa gidajensu, tare da takaitaccen damar samun ababen more rayuwa da tsaro.
Saurari cikakken rahoton Abdulraz Bello Kaura: