Asalin hoton, Getty Images
ƙungiyar Hamas ta ce ta dakatar da sakin sauran Isra’ilawan da ke hannunta, sai yadda hali ya yi.
Sanarwar da bangaren sojin Hamas din ya fitar ta ce “fiye da mako uku, shugabacin ƙungiyar na bibiyar yadda maƙiya suka gaza cika ka’idojin yarjejeniyar da suka cimma”, a cewar Hamas din.
“Karya wannan ƙa’ida, har da jinkirta dawowar wadanda suka rasa muhallansu zuwa arewacin Gaza, inda ake fakon su tare da harbin su, da harba musu bama-bamai, a yankuna daban-daban na Gaza, wanda hakan ke nuni da yadda suka gaza ƙyale ayyukan jinƙai, da sauran yarjejeniyar da suka cimma tunda farko.
“Baya ga nan, dakarun na Hamas tun farko sun mutunta wannan alkawari da aka yi.
Haka kuma sanarwa ta Hamas ta ce “sakin ƙarin wasu masu rajin kafa kasar Yahudawa a ranar Asabar, 25 ga watan 2025, sun dakatar da shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran maƙiya, za su fara mutunta yarjejeniyar da aka cimma da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata.
“Muna sake jadada aniyarmu ta ci gaba da mutunta dukkan yarjejeniya da ka’idojin da aka gindaya, idan har masu mamayar suka bi su sau da kafa”.
An shirya sakin ƙarin wasu Isra’ilawa uku a ranar Asabar.