Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i

Asalin hoton, fb/Nasir El-Rufa’i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa duk da cewa jam’iyyarsa ta APC ta “bar manufofinta na asali”, ba zai taɓa komawa babbar jam’iyyar adawa ta ƙasar, wato PDP ba.

El-Rufa’i ya bayyana hakan a tattaunawar da ya yi da kafar talabijin ta Arise, a yau Litinin.

Tsohon gwamnan, wanda sananne ne a Najeriya, an riƙa raɗe-raɗi game da makomar siyasarsa bayan sukar da ya riƙa yi wa jam’iyyar APC mai mulki.

A lokacin tattaunawar, El-Rufa’i ya nanata sukar da yake yi wa jam’iyyar ta APC, inda ya ce “tambayar da nake yi ita ce me ya sa APC ta manta da manufofin da aka kafa ta a kai?”

“Ban rabu da APC ba, amma APC ta bar ni,” in ji tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Gwamnan ya kuma kore raɗe-radin cewa zai shiga ɗaya daga cikin jam’iyyun adawa na ƙasar, musamman ma jam’iyyar PDP.

“Ya kamata a sani cewa duk da ina APC, ba haramun ba ne na ziyarci wasu abokaina da ke wasu jam’iyyun.”

“Amma babu ko shakka, abin da nake so a sani shi ne ba zan taɓa shiga PDP ba, har abada, na yanke wannan shawarar tuntuni, kuma tun daga wancan lokacin PDP ma ƙara lalacewa ta yi.”

Malam Nasir El-Rufa’i, wanda mutum ne mai yawan tayar da ƙura a siyasasar Najeriya, ya tabbatar da cewa ba zai fita daga harkokin siyasa ba duk kuwa da cewa ya ja baya daga jam’iyyarsa ta APC.

“Ban shirya fita daga siyasa ba, amma nan ba da jimawa ba dole zan nemi inda zan ci gaba da fafutikar cimma ƙudurorina na ci gaba, sai dai ina fatan APC za ta gyara lamurranta, ƙila idan ta gyara ire-iren mu za su sake duba matsayar da muka ɗauka.”

By Ibrahim