Shugabar ƙungiyar agaji ta Red Cross, wato ICRC, ta bayyana cewa halin da ake ciki a Gaza ya zarta azabar jahannama.
A hirarta da BBC, a shalkwatar ƙungiyar da ke birnin Geneva, Mirjana Spoljaric ta ce matsalar ”jin ƙai na ƙara ta’azzara”, yayin da take ganin masifun yaƙin Gaza.
BBC ta tambayi Ms Spoljaric game da kalaman da ta yi cikin watan Afrilu cewa Gaza ce ”jahannamar duniya”, ko a yanzu ta sauya matsayarta?
“Ai lamarin ya ma zarta hakan… Bai kamata mu zura ido muna ci gaba da ganin abin da ke faruwa ba. Lamarin ya wuce hankali da shari’a da tunanin ɗan’adam, la’akari da girman yadda aka ruguza yankin da yawan wahalar da aka jefa mutane”.
“Abu mafi muhimmanci shi ne, ganin yadda aka hana wa mutane kimarsu ta ɗan’adamtaka. Abin yana tayar da hankalinmu.”
Ta ƙara da cewa dole ne ƙasashe su yi duk mai yiwuwa domin kawo ƙarshen yaƙin, da ƙarshen wahalar da Falasɗinawa ke ciki da kuma sakin Isra’ilawan da ake garkuwa da su.
ICRC ƙungiyar agaji ce ta duniya da ta kwashe kusan shekara 150 tana aikin kawar da wahalhalun da yaƙi ya samar a faɗin duniya.