Umar Dikko Radda

Asalin hoton, Umar Dikko Radda

Gwamnatin jihar Katsina ta ce sojojin Najeriya sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗanbindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu’azu, ya bayyana, cewa Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Ya ce, “sojojin saman Najeriya ne suka kai harin ta sama a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Kankara, inda suka samu nasarar ceto mutum 76 ciki har da mata da ƙananan yara.”

Kwamishinan ya bayyana cewa tsaunin ne babban sansani da maɓoyar ɗanbindigar, inda suke shirya kai hare-hare zuwa garuruwa.

Sai dai kwamishinan ya ce wani ƙaramin yaro ya rasu, sannan ya ƙara da cewa nasarar da aka samu na cikin yunƙurin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.

A ƙarshe, ya yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewar da su ke yi wajen gudanar da aiki ba tare da gajiyawa ba.

By Ibrahim

Tu as manqué