...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ƙungiyar Transparency International ta fitar da rahotonta na ayyukan cin hanci da rashawa a duniya a shekara ta 2024, wato Corruption Perception Index.

Rahoton ya yi nazari ne kan ƙasashe 180 bisa la’akari da hujjojin masana da ƴan kasuwa kan matsalar rashawa na kowace ƙasa.

Haka nan rahoton ya dogara da majiyoyi 13 masu zaman kansu domin ɗora ƙasashen kan mizani daga sifili zuwa 100; sifili na nufin matsalar rashawa ta yi muni sosai yayin da 100 ke nufin babu matsalar baki ɗaya.

Rahoton ya ƙara fito da bambancin da ke tsakanin ƙasashen da ke bin tafarkin dimokuraɗiyya da kuma waɗanda ke bin tsari na kama-karya.

Ƙasashen da suke da sauƙin cin hanci a duniya

Mafi yawan ƙasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne.

Bakwai daga cikin ƙasashen 10 na farko, waɗanda ba su da matsalar rashawa duk a yankin Tarayyar ta Turai suke.

Ƙasar da ta fi kowace a duniya samun maki a ɓangaren yaƙi da rashawa ita ce Denmark, wadda take da maki 90.

Sai kuma Finland mai maki 88, ta uku kuma ita ce Singapore, wadda ke a kudu maso gabashin nahiyar Asiya.

Ga yadda ƙasashen 10 na farko suka kasance:

Rahoton na Transparency International ya ce duk da cewa ƙasashen Turai su ne suka fi samun yabo a rahoton, to amma makin da suke samu ya ragu cikin shekara biyu a jere.

Rahoton ya ce wasu shugabannin ƙasashen na Turai sun mayar da hankali wajen “abin da zai daɗaɗa wa harkar kasuwanci kawai a maimakon abubuwan da za su inganta rayuwar al’umma”.

Ƙasashen da ke kurar-baya

Rahoton ya nuna cewa akasarin ƙasashen da ke ƙasan jadawalin suna a nahiyar Afirka ne, inda nahiyar ke da ƙasashe shida cikin 10 da suka samu maki mafi ƙaranci.

Sauran ƙasashen sun fito ne daga nahiyar Amurka ta kudu sai kuma Gabas ta Takiyya.

Sudan ta Kudu da Somaliya su ne ƙasashen da ke ƙasan tebur, inda Sudan ta Kudu ke da maki 8 kacal yayin da Somaliya ke da maki 9.

173. Equatorial Guinea – Maki 13

180. Sudan ta Kudu – Maki 8

Rahoton ya ce nahiyar Afirka, kudu da hamadar sahara ce ta samu maki mafi ƙaranci. Hakan ya faru ne sanadiyyar rikice-rikice masu alaƙa da sauyin yanayi waɗanda ke tarnaƙi ga ci gaban yankin.

Sai dai rahoton ya ce bunƙasar yaƙi da rashawa a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Amurka wani abu ne na farin ciki, sai dai wannan ne karo na farko da aka samu haka a cikin shekara 10, kuma ci gaban da maki ɗaya ne kacal.

Mene ne matsayin Najeriya da Nijar da Ghana?

A tsakanin Najeriya da Nijar da Ghana, Ghana ce ta fi taɓuka abin kirki, inda take a matsayi na 80 bayan samun maki 40.

Sai Jamhuriyar Nijar, wadda take a matsayi na 107 bayan samun maki 34.

Najeriya na a matsayi na 140 inda ta samu maki 26, tare da wasu ƙasashen kamar Mexico da Iraq da Kamaru.

By Ibrahim