- Marubuci, BBC Arabic
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service News
A tsawon shekara goma, Abu Mohammad na rayuwa ne da iyalinsa a arewacin Syria, waɗanda yaƙi ya raba da gidajensu.
Bayan kasa samun kuɗin da za su wadace shi da iyalinsa, kamar wasu ɗaruruwa, ya yanke shawarar tsallaka Turkiyya zuwa Nijar domin aiki a matsayin sojan haya.
Abu Mohammad (ba sunansa na asali ba, shekarunsa 33, matarsa tana da ƴaƴa huɗu – ba su da ruwa da ko banɗaki kuma ba lantarki.
Wurin da suka fake na tanti akwai zafi lokacin bazara da kuma tsananin sanyi lokacin hunturu, kuma ruwa na yoyo lokacin damina.
“Samun aiki da matuƙar wahala,” a cewarsa. Yana cikin ƴantawaye da Turkiya ke mara wa baya waɗanda ke faɗa da shugaban Syria Bashar al-Assad tsawon shekara goma.
Ɓangaren da yake yi wa aiki suna biyanshi dala 50 a wata, amma lokacin da aka yi masa tayin dala 1,500 a wata domin aiki a Nijar, bai yi jinkiri ba ya amince domin zai samu kuɗi.
Ya ce shugabannin ɓangarorin Syria ne suka taimaka wajen tabbatar da samun aikin kuma “bayan cire haraji na dillalai” abin da zai rage masa ba zai wuce kashi biyu bisa uku ba na kuɗin.
“Idan na mutu a fagen yaƙi (a Nijar) za a biya iyalina diyyar dala 50,000,” a cewarsa.
Rikici a yankin Sahel na Yammacin Afirka ya ƙazanta a ƴan shekarun nan sakamakon ayyukan ƙungiyoyi masu da’awar jihadi.
Rikicin ya shafi Nijar da Mali da Burkina Faso – dukkanin ƙasashen uku sojoji sun yi juyin mulki, a ƴan shekarun nan, saboda rashin zaman lafiya a ƙasashen.
Ba Abu Mohammad ne kaɗai ba ke son zuwa Nijar
Ali (ba asalin sunansa ba ne) wanda ke rayuwa a matsugunin ƴan gudun hijira a Idlib yana cikin ƴantawayen Syria tsawon shekara 10 tun yana ɗan shekara 15.
Ya ce shi ma ana biyansa ƙasa da dala 50 a wata, wanda a cikin kwana biyar yake kashe su.
Ya ce dole sai ya nemi rance domin ciyar da iyalinsa kuma yanzu batun Nijar wata babbar dama ce domin samun kuɗin da zai biya bashin da ake binsa.
“Ina son yin ritaya daga aikin soja, domin fara sana’a.” In ji shi.
A nasa ɓangaren kuma Raed (ba asalin sunansa ba ne), ɗan shekara 22 shi ma ɗantawayen Syria ne kuma ya ce zuwa Nijar wata dama ce ta samun kuɗin tafiyar da rayuwarsa da cika burinsa na “aure da kuma samun iyali.”
Tun watan Disamban 2023, sama da mayaƙan Syria 1,000 ne suka tafi Nijar daga Turkiya, a cewar ƙungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria ta Birtaniya (SOHR).
Za su shafe wata shida, kuma tuni har wasunsu sun tsawaita kwangilar zuwa shekara.
Tasirin Turkiyya
Amma sun tafi ne da nufin kare ayyukan Turkiyya da kuma muradunta a Nijar.
Turkiyya ta ƙarfafa tasirinta na siyasa da kasuwanci a yankin, inda ta sayar wa Nijar da jirage marar matuka da za su taimaka wa ƙasar yaƙi da mayaƙa masu da’awar jihadi.
Za su kuma kare wuraren haƙar ma’adinai da suka hada da zinari da Yureniyom (Uranium).
Dukkaninsu sun san cewa duk manufar da aka tura su amma kuma abubuwa za su iya sauyawa bayan sun isa Nijar.
Majiyoyi na SOHR da abokan sojojin hayar waɗanda suka yi aiki a Nijar sun shaida wa BBC cewa ƴan Syria sun koma ƙarƙashin ikon Rasha da ke ba su umarnin yaƙi da masu da’awar jihadi a kan iyakokin Nijar da Mali da Burkina Faso.
Sojoji sun hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum shekara ɗaya da ta gabata, kuma tun lokacin sojojin sun yanke alaƙa da ƙasashen yammaci.
“Nijar ta shiga neman sabbin aminai, kuma ta samu Rasha suka ƙulla ƙawance,” kamar yadda Nathaniel Powell wani mai bincike kan yankin Sahel a cibiyar Oxford Analytica ya bayyana.
“Makaman yaƙin Rasha suna da sauƙi fiye da na ƙasashen yammaci. Kuma Rasha na bayar da horo da kuma amincewa da sharuɗɗan ƙasashen ba tare wani sharaɗi ba, saɓanin ƙasashen yammaci.”
Samun damar yaƙi ƙarƙashin umarnin Rasha wani abu ne na daban ga mayaƙan waɗanda ke adawa da gwamnatin Syria, duk da Rasha na da aminci da shugaba Assad.
“Mu sojojin haya ne a nan da can,” a cewar Abu Mohammad, ” Amma yanzu aikin Turkiya nake yi, Ba zan karɓi umarnin Rashawa ba.”
Amma ba ya da zaɓi, kamar yadda Raed ya bayyana. “Na tsani waɗannan dakarun amma dole ce ta sa zan tafi saboda matsalar tattalin arziki,” in ji shi.
Dukkaninsu suna jiran sanya hannu kan yarjejeniyar inda za su yi “kafin su tafi ko kuma a lokacin da suke kan hanya,” a cewar Raed.
Ya bayyana cewa a asirce ake yin tsarin kuma ya san wanda shugabannin ƴantawayen Syria suka ɗaure saboda ya kwarmata bayanan aikin sojan haya da za su tafi a Afirka.
Daga cikinsu da muka tattauna da su sun ce shugabanninsu sun shaida masu cewa wani kamfanin Turkiyya da ake kira SADAT ne zai kula da su da zarar sun amince da kwangilar wanda zai ɗauki ɗawainiyarsu.
Shekara biyar da suka gabata, Abu Mohamad ya tafi Libya inda ya yi aiki a matsayin sojan haya na tsawon wata shida kuma ya yi iƙirarin cewa kamfanin SADAT ne ya ɗauki nauyi.
Ƙungiyar SOHR ta yi iƙirarin cewa daga bayanan da ta samu daga sojojin hayar da suka riga suka isa Nijar, SADAT ne ya ɗauki nauyinsu.
Ba za mu iya tabbatar da wannan iƙirarin ba. Mun tuntuɓi SADAT, amma kamfanin ya musanta ɗaukar sojojin hayar Syria zuwa Nijar, yana mai cewa “iƙirarin san ba gaskiya ba ne… babu wani aiki da muke yi a Nijar. ”
Kamfanin ya kuma ce babu wani aiki da yake yi a Libya idan ba aikin wasanni ba na soja da ya shafe shekaru 10 wanda rikici ya sa ya janye.
Kamfanin ya ƙara da cewa “Ba ya da wata alaƙa na samar da taimako ga wasu masu zaman kansu, amma yana bayar da shawarwari da horo da kuma kula da hidimar sojoji a fagen daga, ƙarƙashin dokokin Turkiyya.
Amma ana amfani da kamfanoni masu zaman kansu a Ankara wajen ɗaukar sojojin haya da kuma tura su zuwa Nijar, a cewar ƙungiyar SOHR. Daraktan ƙungiyar Rami Abdul Rahman, ya zargi gwamnatin Turkiya da fataucin ƴan Syria da kuma alƙawalin ba su kuɗi.
Amma BBC ta miƙa waɗannan zarge-zargen ga ma’aikatar harakokin wajen Turkiyya, amma babu wata amsa.
Ba wannan ne karon farko da ake zargin gwamnatin Turkiyya da tura mayaka daga Syria ba zuwa wata ƙasa.
Rahotanni da dama da suka haɗa da na ma’aikatar tsaron Amurka sun tattara bayanai kan mayakan Syria da ke samun goyon bayan Turkiyya da ke faɗa a Libya.
Turkiyya a baya ta yarda cewa akwai mayaka na Syria a Libya amma ba ita ce ta tura su ba.
Turkiyya ta kuma musanta tura sojojin haya na Syria zuwa yankin Nagorno-Karabakh da ake taƙaddama.
Rayuwa a Nijar
Yanayin rayuwa a Nijar na nufin, tuntuɓar iyali a Syria zai yi wahala. Lokacin da sojojin hayar suka isa za a ƙwace wayoyinsu, a cewar Abdul Rahman na ƙungiyar SOHR. Kuma Abu Mohammad ya ce abokansa a Afirka “suna tuntuɓar iyalansu ne sau ɗaya duk mako biyu, wani lokaci ma ƙasa da haka.”
Ya ƙara da cewa ba su iya magana da matansu ko iyayensu, kuma dole sai da amincewar shugabanninsu a Nijar sannan za su iya sadarwa. “Wadanda ke tabbatar wa iyalan cewa suna nan lafiya lau.”
Ali ya ƙara da cewa wasu abokansa da suka tafi Nijar sun ce suna shafe lokacinsu ne a cikin sansanonin soji, suna jiran umarnin su yi tafi fagen daga.”
Kuma ba dukkaninsu ba ne ke komawa gida. Kungiyar SOHR ta ce an kashe tara a Nijar sun Disamban 2023. An tafi da gawar huɗu daga cikinsu amma ba a tantance su ba.
Raed da Ali sun ce iyalansu ba su son su tafi, daga ƙarshe ƙarya za su yi cewa za su tafi Turkiya domin samun horo na wasu watanni.
Iyalan Abu Mohammad su ma ba su yarda da tafiyar ba. “Idan da ina da sukunin yin rayuwar wadata, ba zan yi wannan aikin ba ko waɗanne miliyoyin daloli ne za a ba ni,” a cewarsa. Amma ya ce “yaronsa ya buƙaci ya saya masa keke, wanda ba ya da ƙarfin saya – irin haka ke zuga ni dole na tafi.”
An sauya sunayen Abu Mohammad da Ali da Raed saboda dalilai na tsaro