Janar Abdourahamane Tchiani
Janar Abdourahamane Tchiani

Masana da masu ruwa a tsaki da gwamnatin mulkin soji ta Jamhuriyar Nijar ta tara domin tsara makomar ƙasar sun kammala taron ƙasa da suka kwashe kwana biyar suna gudanarwa. Taron ya fara ne daga ranar Asabar 15 ga watan Fabarairu, zuwa Alhamis 20 ga watan na Fabarairu. Shugaban mulkin soji na ƙasar Abdourahamane Tchiani ne ya kira taron domin seta hanyar da ƙasar za ta bi a shekaru masu zuwa.

Tun farko, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi wa Mohammed Bazoum, gwamnatin sojin ta Nijar ta nuna alamun cewa za ta iya mayar da mulki ga farar hula cikin shekara uku, sai dai sakamakon taron ƙasar ya nuna akasin haka.

Tabbatar da Tchina a matsayin shugaban ƙasa

Taron haɗin kan ƙasar na Jamhuriyar Nijar ya amince da sauya yadda ake kiran jagoran juyin mulkin ƙasar zuwa ‘shugaban ƙasa’. Taron ya ce ya cimma matsayar ne bayan la’akari da “jagorancin” da Tchiani ya nuna wajen sake ƙwato wa Nijar “ƴancinta”.

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta shekara biyar

Taron ƙasar ta Jamhuriyar Nijar ya amince da samar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta tsawon shekara biyar, wadda ita ce za ta tsara yadda za a mayar da ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya. A lokacin gabatar da jawabi kan matsayar da taron ya cimma, ɗaya daga cikin jagororin taron, Bibata Niandou ta ce: “Miƙa mulki zai kasance a cikin wata 60, wato shekara biyar, daga ranar da aka amince da wannan tsari.” Sai dai ta ƙara da bayanin cewa wa’adin da aka ɗiba na mayar da mulkin ga farar hula zai iya “sauyawa” bisa la’akari da “yanayin tsaro” a ƙasar.

Takara

Taron ya yarda cewa jagororin mulkin sojin ƙasar za su iya tsayawa takara a zaɓen da za a gudanar bayan shekara biyar na riƙon ƙwarya. Hakan na nufin shugaban mulkin soji na ƙasar a yanzu na da damar tsayawa takara. Wannan na daga cikin ɗabi’un shugabannin mulkin soji a nahiyar Afirka, inda sojojin da suka yi juyin mulki kan rikiɗe zuwa shugabannin farar hula ta hanyar zaɓe.

Ƙara wa Tchiani muƙami

Ɗaya daga cikin mataimakan shugaban taron, Abdoulaye Seydou ya kuma bayyana cewa taron ya amince da ƙara wa shugaban mulkin soji na ƙasar Abdourahamane Tchiani daga Birgediya-Janar zuwa Janar na soja. A yanzu dai za a gabatar wa majalisar mulkin sojin Jamhuriyar Nijar matsayra da taron ya cimma domin amincewa tare da ɗaukar matsaya ta ƙarshe. Taron ya ƙunshi mutane kimanin 700, waɗanda suka fito daga ɓangarori da dama na ƙasar, da suka haɗa da tsofaffin ministoci da masana da lauyoyi da sojoji da malamai da kuma ƴan ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin ƙasashe uku – Burkina Faso, Mali da Nijar – waɗanda suka tsame kansu daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, tun bayan juyin mulkin soji da suka faru a ƙasashen. Haka nan sun raba-gari da ƙasashen yammacin duniya, ciki har da uwar-gijiyarsu, Faransa, sannan suka karkata alaƙarsu zuwa Rasha.

By Ibrahim