Asalin hoton: Facebook/Atiku Abubakar
Wells Carlton Hotel and Apartments da ke Asokoro, Abuja, ya soke wani taron domin ƙaddamar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandalin haɗin kan jam’iyyun adawa a Najeriya.
A safiyar ranar Laraba, otal ɗin ya ce wannan soke taron ya biyo bayan wani “batun bin doka na cikin gida” ba tare da bayyana dalilin soke taron dalla-dalla ba.
A cikin wani saƙo da otal ɗin ya aika, wanda ɗan jarida Dele Momodu ya wallafa a shafinsa na Instagram, otal ɗin ya ce ba haka zancen yake ba.
“Muna matuƙar bakin ciki da sanar da ku cewa, saboda wani batun bin doka da muka gano yanzu, ba za mu iya ci gaba da karɓar taronku da aka shirya ba.”
“Mun fahimci cewa saura ƙasa da awanni 24 taron ya gudana, kuma muna ba da haƙuri sosai bisa wannan jinkiri da ƙalubalen da hakan ka iya jawo muku.”
Wannan lamari ya haifar da ƙarin ce-ce-ku-ce daga ’yan adawa, inda aka zargi gwamnati da tsoratarwa da katsalandan.
Taron ADC na da nufin haɗa manyan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da Atiku Abubakar, David Mark, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, da sauran tsofaffin gwamnoni da ministoci.