Asalin hoton, Getty Images
Kafar yaɗa labarai ta BBC da wasu kafafen yada labarai uku sun nuna damuwa kan ƴan jarida da ke aiki a Gaza, waɗanda suka ce na shan wahalar samun abin ci.
Waɗanda ke aiko da rahotanni kan rikicin na Gaza na fuskantar yunwa “kamar sauran mutanen da ke yankin,” in ji wata sanarwa da BBC ta fitar tare da kamfanin dillacin labarai na Faransa (AFP), na Amurka (AP), da Reuters na Birtaniya.
“A tsawon watanni, waɗannan ƴan jarida masu zaman kansu sun kasance idanu da kunnuwan duniya a Gaza”, a cewar sanarwar.
Kafafen yaɗa labarai na ƙasar waje suna dogara ne da ƴan jarida na cikin gida a Gaza, kasancewar Isra’ila ta haramta wa kafafen yada labarai, ciki har da BBC, tura wakilansu zuwa Gaza.
Hakan na zuwa ne yayin da sama da ƙungiyoyin bayar da agaji 100 da na kare hakkin bil’adama suka yi gargaɗin cewa akwai barazanar samun mummunan hali a Gaza saboda yunwa.
Sai dai Isra’ila, wadda ke iko da hanyoyin shigar da agaji a Gaza, ta zargi ƙungiyoyin da “yaɗa farfagandar Hamas.”
Falasɗinawa 45 ne suka mutu sanadiyyar yunwa tun daga ranar Lahadin da ta gabata a yankin, kamar yadda ma’aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas ta bayyana.