Asalin hoton, Reuters

‘Yar takarar jam’iyya mai mulki a Namibia, Swapo, Netumbo Nandi-Ndaitwah, ta zama mace ta farko da aka zaɓa shugabar ƙasar a zaɓen makon da ya gabata wanda ake taƙaddama a kansa.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce Nandi-Ndaitwah mai shekara 72, ta samu sama da kashi 57 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa inda ɗan takara mafi kusa da ita, Panduleni Itula ya samu kashi 26 cikin ɗari.

Nandi-Ndaitwah, wadda ita ce mataimakiyar shugaban ƙasar a yanzu, da wannan nasara za ta kasanace shugaba ta biyar kenan tun bayan da ƙasar ta yankin kudancin Afirka ta samu ‘yancin kai a 1990.

Kuma jam’iyyarta, Swapo, ita ce ke mulki tun daga samun ‘yancin har yanzu.

Sakamakon matsalolin da aka gamu da su na kayan aiki da kuma ƙarin kwana uku da aka yi a zaɓen a wasu sassan ƙasar, Itula ya yi zargin an yi maguɗi a zaɓen.

Yawancin jam’iyyun hamayya sun ƙaurace wa wajen bayyana sakamakon zaɓen a jiya Talata da daddare, a babban birnin ƙasar Windhoek.

Idan aka rantsar da ita za ta zama mace ta biyu kenan da ke shugabanci a Afirka, inda a yanzu ake da Samia Suluhu Hassan a Tanzania.

By Ibrahim