Asalin hoton, Tinubu/Facebook
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta amince tare da bayar da goyon bayanta ga salon mulkin Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a lokacin taron ƙolinta a yau Laraba a Abuja, inda kuma ta amince shugabanta Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da jan ragamarta.
A yayin taron ne, shugabannin jam’iyyar suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayansu ga yadda shugaban ƙasar ke gudanar da mulki, tare da yabawa da ƙoƙarinsa.
Taron wanda shi ne na ƙoli wajen ɗaukar matsaya game da harkokin jam’iyyar ya mayar da hankali ne kan nazari a game da abubuwan da suka shafi jam’iyyar, da nasarorin da ta samu da kuma ɓangarorin da take buƙatar gyara.
A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce matakin taron kwamitin ƙolin zaburarwa ce ga gwamnatinsa, inda ya yi alƙawarin ƙara zage damtse wajen tafiyar da harkokin ƙasar.
Tinubu wanda ya sha alwashin cewa ba zai ba wa jam’iyyar kunya ba, ya kuma tabbatar da cewa tattalin arziƙin ƙasar na kan hanyar farfaɗowa.
Akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar da ba su halarci taron na yau ba, lamarin da ake alaƙantawa da fushinsu a kan yadda harkokinta ke tafiya.
To amma kuma taron ya tattauna a kan wasu ƴaƴan jam’iyyar, waɗanda ba sa jin daɗin yadda ake gudanar da ita.
Wannan shi ne karon farko da jam’iyyar ta APC ke gudanar da taron ƙolin, tun bayan rantsar da Shugaba Tinubu a watan Mayun 2023.