...

Asalin hoton, BBC Hausa

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasa da ya faru ranar Talata, lokacin da jirgin ya kama hanya daga Abuja zuwa Kaduna.

A tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, Opeifa ya ce za su yi bincike mai zurfi kan abin da ya sanya jirgin ya kauce daga kan layi.

“Bayan neman gafarar ƴan Najeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki cikakken alhakin abin da ya faru,” in ji shi.

Opeifa ya tabbatar da cewa hatsarin bai kamata ya faru ba, amma NRC za ta tabbatar hakan bai sake faruwa ba.

Hatsarin ya faru ne bayan jirgin ya tashi daga Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin ruɗani da tsoro.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta ce hatsarin ya jikkata mutum bakwai, waɗanda suka samu kulawar likitoci.

Jirgin saman Abuja zuwa Kaduna ya yi ƙaurin suna kan samun tangarɗa a kai a kai.

A bara jirgin ya samu tangarɗa a kusa da garin Jere, amma babu wani fasinja da ya jikkata. Hakanan ma a 2023 a kusa da tashar jirgin ƙasa ta Kubwa an sami irin wannan tashin hankali.

Mafi munin tangarɗar da jirgin ya samu a tarihinsa shi ne a shekara ta 2022, lokacin da wasu gungun yan bindiga suka farmaki jirgin tare da yin garkuwa da mutum 60.

An ƙaddamar da sufurin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna mai nisan kilomita 186 a shekara ta 2016, don ba matafiya zaɓi daga bin hanyar mota, lokacin da ake fama da matsalar tsaro ta ƴan bindiga masu tare hanya suna garkuwa da mutane.

By Ibrahim

Tu as manqué