Asalin hoton, X/CAFonline
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayar da tukwicin kuɗi dala 100,000 ga kowanne daga cikin ƴan wasan tawagar Super Falcons, wanda ya kai naira miliyan 153.
Haka nan, kowanne daga cikinsu ya samu kyautar gida mai ɗaki uku, yayin da tawagar masu horaswa ta samu kyautar dala 50,000.
Tinubu ya sanar da hakan a ranar Litinin lokacin da ya tarbi tawagar matan bayan nasarar da suka samu ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na Afirka karo na 10.
A ranar Asabar ne Super Falcons suka lallasa Atlas Lionesses na Morocco da ci uku da biyu a wasan ƙarshe na gasar cin kofin da Moroccon ta karbi baƙunci.
Baya ga kyautar kuɗi da gida, Tinubu ya karrama ƴan wasan da lambar girmamawa ta ƙasa, OON.
Haka nan, ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ba da kyautar kudi naira miliyan 10 ga tawagar Super Falcons.
A lokacin da yake jawabi, Tinubu ya ce: “Na karɓi wannan kofi a madadin ƴan Najeriya, mun gode da wannan ƙwazo, saboda haka na karrama ƴan wasan da masu horas da su da lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON).
“Bugu da ƙari, na bayar da umarnin a bai wa dukkanin ƴan wasa da masu horas da su gidaje masu ɗakuna uku-uku.
“Haka nan, akwai kyautar kudin naira kwatankwacin dala 100,000 ga kowace ƴar wasa 24 da kuma dala 50,000 ga tawagar masu horaswa.”