Volodymyr Zelensky da Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Wani taron manema labarai da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi ya fito da ɓarakar da ke tsakaninsa da Shugaban Amurka Donald Trump, ƙarara.

Haka kuma maganganun da ya yi sun nuna yadda ƙasar ta Ukraine ke dab da rasa Amurka a matsayin ƙawa – har ma wasu na cewa ai tuni sun raba gari.

Kalaman da Shugaba Trump ke faɗi sun yi kusan daidai da abin da gwamnatin Rasha ke faɗa, amma matakin da zai ɗauka ya kawo ƙarshen yaƙin bai bayyana ba har yanzu.

Zelensky ya ce zuwa yanzu yaƙin ya laƙume dala biliyan 320, yana mai ƙara da cewa alƙaluman sun bambanta tsakanin gwamnatinsa da kuma Amurka.

Ya ce kusan dala biliyan 120 ta fito ne daga asusun Ukraine yayin da Amurka da Turai suka bada dala biliyan 200.

Amurka ta ba ta makamai da kuma tallafin kasafin kuɗi da suka kai na dala biliyan 67.

A baya, Trump ya ce Amurka na son abin da yake daidai da dala biliyan 500 na ma’adanan ƙarƙashin ƙasa na Ukraine, idan ƙasar na son Amurka ta ci gaba da ba ta goyon baya da tallafi.

Zelensky ya ce Amurka ta yi zargin cewa tana tallafa wa ƙasarsa da kashi 90 cikin ɗari a yaƙin da take yi – ‘to amma gaskiyar tana wani waje daban,’ in ji shi, ‘to amma muna godiya da taimakonsu.’

By Ibrahim