...

Asalin hoton, INEC

Bayanan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya – INEC – kan alƙaluman makon farko na mutanen da suka yi rajistar zaɓe ta intanet sun nuna cewa al’umma a yankin arewacin ƙasar ba su fito sosai domin yin rajista.

Alƙaluman da INEC ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa jihar Osun ce ta fi yawan masu sha’awar rajistar, da yawan 393,269, yayin da jihar Legas take biye mata da mutum 222,205, sannan jihar Ogun na da yawan masu son yin rajista 132,823.

A arewacin Najeriya, Abuja, babban birnin tarayya, na da mafi yawan masu rajista da mutum 107,683, sai jihar Kaduna da mutum 61,512, yayin da jihar Kogi ke biye mata da mutum 58,546.

Jihar Kano wadda ta fi kowacce yawan al’umma na da mutanen da suka nuna aniyar rajista 10,166, yayin da Adamawa ke da 2,115 kacal.

Duk da haka, idan an duba ƙasar baki ɗaya, za a ga yankin kudu maso gabas shi ne ya fi ƙarancin mutanen da suka yi rajista a makon farko.

Jihar Enugu na da mutum 484, Imo 481, sannan jihar Ebonyi tana da mutum 261 kacal.

A ranar 18 ga watan Agusta ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta buɗe shafinta na intanet domin rajistar katin zaɓe.

Alƙaluman INEC sun nuna cewa, har zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta, an samu mutum miliyan 1,379,342 da suka nuna sha’awarsu yin rajistar ta shafin intanet.

A halin yanzu, alƙaluman INEC sun bayyana cewa mata ne ke gaba a yawan rajistar, suna da kashi 52.04%, yayin da maza ke da kashi 47.96%.

Hukumar ta sanar da cewa ta buɗe rumfunanta a faɗin ƙasar don bai wa mutane damar zuwa ƙafa-da-ƙafa domin yin rajista.

Aikin rajistar zaɓe yana zuwa ne gabanin babban zaɓen shekara ta 2027, inda jam’iyyu da masu neman takara suka fara shiri.

A yanzu haka, Najeriya mai yawan mutum sama da miliyan 200 na da mutanen da suka yi rajistar zaɓe miliyan 93,469,008 a faɗin ƙasar.

...

Asalin hoton, INEC

Ƙa’idojin rajistar zaɓe a Najeriya:

1- Wajibi ne mutum ya kasance ɗan Najeriya

2- Wajibi ne mutum ya kai shekara 18 da haihuwa kafin ranar yin rajista

3- Wanda ya kai shekara 18 amma bai yi rajista ba a baya

4- Wajibi ne ya kasance mazauni, ko ma’aikaci, ko kuma ɗan asalin wata ƙaramar hukuma ko gundumar da aka yi rajistar zaɓe

5- Dole ne babu wani abu na shari’a da ya haramta masa yin zaɓe bisa dokokin Najeriya

6- Dole mutum ya gabatar da kansa a wajen masu aikin rajistar zaɓe don yin rajista tare da shaidar tantancewa, da na shekarar haihuwa idan aka buƙata

7- Idan mutum yana da katin zaɓe amma babu sunansa a rajista, akwai buƙatar ya je domin yin rajista

8- Idan mutum ya fuskanci matsala a lokacin tantancewa a zaɓen da ya gabata, zai je domin yin rajista

By Ibrahim

Tu as manqué