Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi zargin cewa kungiyoyi ‘yan bindiga da kuma dakarun gwamnatoci a yammacin Afrika sun tafka ta’asa ba tare da daukar wani mataki ba a shekara ta 2024.
A rahoton da ta fitar na sabuwar shekara, kungiyar ta Human Rights Watch ta ce dubban mutane sun rasu, wasu kuma an jima musu raunuka amma ba a dauki hukunci ba.
Kungiyar Human Rights Watch ta ce a shekarar ta da wuce, ta yi nazari kan cin zarafin bil’adama a kasashe fiye da 100 a duniya, abin da ya ba ta damar fitar da wannan rahoto.
Rahoton, mai shafi 546, ya nuna cewa a kasashe da dama gwamnatoci sun murkushe masu zana-zanga da karfi, an kama mutane ba tare da sun aika ta laifi ba, sannan an garkame abokan hamayya na siyasa a kurkuku. Tare da cin zarfin ‘yan jarida da masu rajin kare hakkin bil’adama.
Kungiyar ta ce ƴan bindiga da sojojin gwamnati sun kashe fararen hula babu gaira babu dalili, wasu mutanen an raba su da muhallansu.
A cewarta, a kasashe fiye da 70 a bara da aka gudanar da zabe, shugabanni masu kama karya sun kara karfi tare da kafa dokoki na zalunci.
Shugaban Human Rights Watch a Afrika, Mausi Samuel, ya ce akwai bukatar kungiyar tarrayar Afrika AU ta gudanar da bincike kan irin munanan cin zarafin bil’adama da ake yi a nahiyar. A kan Najeriya kuwa, rahoton ya ce akwai rauni game da irin matakan da gwamnati ke dauka wajen hukunci ‘yan bindiga saboda yadda suka raba miliyoyin mutane da muhallansu tare da kashe daruruwan mutane.
Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce sauye-sauyen tattalin arziki a Najeriya sun jawo mummunan talaucin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 30, kuma babu wani tsari na hakika da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, sai ma ta yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen hana zanga-zangar tsadar rayuwa.
Rahoton kungiyar kuma ya taɓo irin ta’asar da aka tafka na cin zarafin bil’adama a kasashen Guinea, Mali, Nijar da Burkina Faso, wanda ke nuna irin gwamnatocin da ke shugabanci a yankunan.