Gwamnan jihar Kaduna

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric da ke da alhakin samar da lantarki ga jihohin Kaduna, Kebbi, Sokoto da Zamfara ya ce an gaza cimma matsaya tsakanin shugabannin kamfanin da kungiyar ma’aikatan, duk da sanya bakin gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Babban Jami’in sadarwar kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, a cikin wata sanarwa ya ce duk da ƙoƙarin samun matsaya, ma’aikatan sun ƙi amincewa su maido da wutar lantarki bayan katse ta tun ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu.

Ya ce an gudanar da taruka tare da hukumomin tsaro da Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Uba Sani, wanda mataimakiyarsa Hadiza Balarabe ta wakilta, inda aka bayyana tasirin rashin wutar akan fannin lafiya da kasuwanci, tare da bukatar mayar da wutar a lokaci.

A cewar sanarwar, an kuma yi zaman shiga tare da babban lauyan Najeriya Sani Katu da kwamishinan shari’ah na jihar Kaduna Sule Shuaibu SAN, sai dai haƙar ta gaza cimma ruwa sakamakon sabbin buƙatu da ƙungiyar ma’aikatan ta gabatar.

Abdulazeez ya kuma ce: “Wannan mataki da suka ɗauka ya saɓa wa tabbacin da suka bai wa gwamnatin jihar Kaduna tun da farko na cewa za su mayar da wutar lantarkin a yayin da ake cigaba da tattaunawa.”

A farkon makon nan ne dai Kamfanin rarraba wutar lantarkin na Kaduna Electric ya ce ya sallami ma’aikata fiye da ɗari huɗu, wanda hakan ya kai ga shiga yajin aikin ma’aikatan tare da jefa alummomin jihohi huɗu cikin duhu.

Lamarin ya jefa al’umma cikin ƙunci da haifar da asara ga masu sana’o’i.

By Ibrahim