Asalin hoton, XnatashaAkpoti
Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar dattajai, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna.
Natasha ta shigar da karar ne gaban babbar kotun tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa, Mfon Patrick.
Ta nemi kotun tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara.
Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya bayyana cewa kalaman da babban mai taimaka wa shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya wallafa a shafinsa na facebook sun ɓata mata suna.
Barista Giwa ya yi zargin cewa kalaman ba komai ba ne illa ɓata suna, tsokanar fada, da ƙanskantar da ita a idon abokan aikinta da sauran al’umma.
Sanata Natasha ta bukaci kotun da ta haramta wa waɗanda ake ƙara ko makusantansu daga wallafa duk wani rubutu na batanci a game da ita.
A makon da ya gabata, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwarta kan yadda aka bai wa wani dan majalisa wurin zamanta, saboda wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman majalisar. Inda ta ki amincewa da sauyin wajen zaman da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ta da shugaban majalisar dattawan.
Tuni aka umarci kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawan da ya gayyaci Sanata Natasha don bin bahasi kan rikicin sauyin wajen zaman.