Soji
Asalin hoton, DEFENCE HQ/X

Dakarun haɗin gwiwa na jami’an tsaron Najeriya da suke aiki na musamman na Fansan Yamma sun mayar da martani kan harin da sojoji suka kai, wanda ya yi ajalin mutane a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

A jiya Laraba ne wasu hare-haren da sojojin Najeriya suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto suka yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 10 da raunata wasu da dama.

A wata sanarwa da kakakin aikin sojin, Laftanar kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, kan zargin sojoji da kai wa farareb hula, ya ce sun kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri.

“Sojoji ba sa ƙaddamar da hare-hare yi sai an tattara bayanan sirri, musamman hari kan ƴanta’adda irin su Lakurawa, saboda dole a tabbatar harin ya kai gare su.”

“Ya kamata mutane su riƙa tantance bayanai domin gudun yaɗa labaran ƙarya tare da jefa tsoro a zuƙatan mutane. Akwai yiwuwar ƴanta’addan za su yi na amfani da yaɗa labaran ƙarya domin kawo tsaiko ga aikin sojin.”

Ya ƙara da cewa, “yankunan Gidan Sama da Rumtuwa da aka kai hare-haren, yankuna ne da aka gano akwai ƴan Lakurawa.”

By Ibrahim