Babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya ce jami’an rundunar sun kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban har mutum 30,313, sannan sun ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250 a shekarar 2024.
Shugaban ƴansandan ya bayyana haka ne a taron ganawa manema labarai a ranar Talata, 24 ga watan Disamba a Abuja.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ya ce sun bayyana nasarar da suka samu ne domin nuna irin shirin fuskantar baɗi da suke yi.
Shugaban ƴansandan ya yaba da ƙokarin jami’ansa da sadaukarwar da suka yi a shekarar, inda ya ƙara da cewa an samu nasarar ce tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, wanda ya nuna ƙoƙarinsu na tabbatar da tsaro mai inganci.
“Rundunar ƴansandan Najeriya ta samu nasarar daƙile masu aikata laifuka, inda ta samu nasarar kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban guda 30,313 da ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250, sannan mun ceci waɗanda aka yi garkuwa da su guda 1,581.”
Ya kuma yi kira ga hafsoshin rundunar su riƙa amfani da kimiyyar zamani domin aikinsu ya ƙara nagarta.