A cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako, mun kawo muku tattaunawa da Amir Iliyasu (Mai Rose), wanda aka fi sani da Garzali a cikin shirin Daɗin Kowa.
Amir, wanda darakta ne, ya kuma shirya finafinai da dama tare da tsohon tauraron Kannywood, Rabilu Musa (Ibro).