Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT PRESS

Kotun Ƙolin Najeriya ta umarci babban akanta da babban bankin ƙasar wato CBN na Najeriya da su dakatar da kason kuɗin jihar Rivers, har sai gwamnan jihar ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban halastacciyar majalisar jihar.

Alƙalan kotun su biyar ne suka yanke wannan hukuncin, inda kotun ta ce Martins Amaewhule ne sahihin shugaban majalisar.

Wannan ya kawo ƙarshen lokaci mai tsawo da aka ɗauka ana shari’a tsakanin ɓangarorin biyu kan rikita-rikitar siyasa a jihar.

Haka kuma ana ganin wannan matakin a matsayin wata nasara ga ɓangaren Ministan Abuja, Nyesome Wike, kan Gwamnan jihar, Sim Fubara.

Mai shari’a Emmanuel Agim ne ya karanta hukuncin, inda ya ce, “muna umartar Babban Bankin Najeriya CBN da Babban Akanta na Najeriya da su dakata da tura kuɗin kason jihar Rivers har sai gwamnan ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban majalisar jihar ƙarƙashin Martin Amaewhule,” kamar yadda ya bayyana.

A gefe guda kuma, a wata shari’ar daban, kotun ƙolin ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka yi a ranar 5 ga Oktoban 2024.

Mai shari’a Jamilu Tukur, ya ce zaɓen wanda hukumar zaɓen Rivers mai zaman kanta ta shirya, ya saɓa da sashe na 150 na kundin tsarin zaɓe na ƙasar.

By Ibrahim