Asalin hoton, Tangaza
Akwai zargin cewa mambobin ƙungiyar Lakurawa sun kashe mutum 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya a ƙaramar hukumar Tangaza, jihar Sokoto.
Harin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.
Ana zargin harin martani ne bayan kashe wasu mutum uku daga cikin kungiyar, ciki har da wanda ake zargin shugabansu a wani harin da ya faru a baya a garin.
Ɗaya daga cikin shugabannin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa maharan sun taru a ƙauyen lokacin da jama’a ke cikin masallaci suna gudanar da sallar Azahar.
“Muna cikin masallaci lokacin da suka kai hari da yawansu.”
“Da zuwansu suka fara harbe-harbe,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba domin halartar jana’izar waɗanda aka kashe.
“Wannan shine karo na farko da ƴan Lakurawa suka kai hari kai tsaye a garinmu.
“Amma na yi tunanin martani ne bayan kashe wasu daga cikinsu a wani harin da ya faru a baya,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun ƙone gonaki da gidaje da dama tare da lalata wata ariya ta sadarwa.
Asalin hoton, Tangaza