Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Chérif Ousman MBARDOUNKA
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journaliste-BBC Afrique
- Twitter,
Nijar za ta gudanar da taron ƙasa daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Fabarairu. Ana sa ran taron ya sanya lokacin mayar da mulki hannun farar hula bayan hamɓarar da gwamnatin dimokuraɗiyya ta Mohamed Bazoum a 2023. Jim kaɗan bayan juyin mulkin da ya yi, Janar Abdourahmane Tchiani ya sanar da shirin yin taron ƙasa wanda zai fayyace abubuwan da gwamnati za ta fi mayar da hankali a kai da kuma sanya wa’adin mayar da ƙasar mulkin farar hula.
Haka kuma a lokacin ya sanya wa’adin mayar da ƙasar mulkin dimokuraɗiyya cikin wa’adin shekara uku to amma tun bayan nan bai ƙara magana a kai ba. A farkon 2024, an gudanar da tarukan tuntuɓa a yankuna takwas na ƙasar. Wannan tuntuɓa da aka yi ita ce za ta zama jigo na taron ƙasa da za a yi a Yamai a mako mai zuwa.
‘Sake gina ƙasar’

Asalin hoton, Getty Images
Ma’aiakatar kula da harkokin cikin gida ce ta sanar da ranakun zaman a wata sanarwa da aka karanta a tashar talabijin ta ƙasar a ranar Asabar da daddare. An kafa wata hukuma ta ƙasa da za ta shirya taron, inda za ta mika rahotonta na ƙarshe ga Janar Tchiani a farkon watan Maris. Rahoto na ƙarshe wanda kuma zai yanke shawara kan ko Janar ɗin zai iya tsayawa takara a zaɓe nan gaba.
Hukumar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Dr Mamoudou Harouna Djingareye, sarkin Sinder da ke yankin Tillabéri, tana da mataimakan shugaba guda bakwai. Ta haɗa da tsohon Firaminista Ibrahim Assane Mayaki, da tsofaffin ministoci da dama, da malaman jami’a, da lauyoyi, da jami’an soji, da masu bayar da shawara ga Janar Tchiani, da shugabannin addini, da jagororin ƙungiyoyin farar hula.
Hukumomi sun ce wannan wakilci ne na al’ummar Nijar, yayin da ya rage wa hukumar mako uku ta mika rahotonta na ƙarshe, an karkasa ta zuwa ƙananan kwamitoci biyar domin aiki a kan waɗannan muhimman batutuwan:
- Zaman lafiya da tsaro da sasanci da kuma haɗin kai a ƙasa
- Sake tsari da inganta harsashin siyasa da hukumomin ƙasar
- Tattalin arziƙi da samar da cigaba mai ɗorewa
- Siyasar yanki da alaƙa da ƙasashen waje
- Shari’a da ƴancin ɗan’adam
Babban aikin hukumar ya haɗa da samar da daftarin tsarin mayar da ƙasar kan mulkin dimokuraɗiyya tare da tsara shawarwarin da taron ya tattara. Haka kuma hukumar ce ke da alhakin samar da tsarin sadarwa ga ƙasashen duniya domin samun goyon baya ga shirin. Tahirou Guimba, mamba a hukumar da ke jagorantar waɗannan taruka ya ce babu wai abu da za a kauce tattaunawa a kai a taron.
Ya bayyana fatansa na cewa aikin da za su yi zai kai ga tattara muhimman abubuwa da ke ci ma ‘yan ƙasar tuwo a ƙwarya.
Gaggan da ba sa cikin tsarin taron
Jumulla akwai mutum 674 da suka haɗa da ‘yansiyasa da ƙungiyoyin farar hula da shugabannin gargajiya da na addini da jami’an tsaro da ƙwararru a kan tsaro da za su halarci taron na kwana biyar. To sai dai kuma ba a gayyaci ainahin jam’iyyun siyasa da a hukumance suke ƙasar ba, wajen wannan taro, abin da ya janyo suka daga jama’a a kan halarcin wannan taro na ƙasa. Babu ko da ɗaya daga cikin jam’iyyun siyasar ƙasar masu rijista 172 da aka gayyata taron.
Tsarin haɗakar ƙasashen Sahel – AES
Sabuwar dokar 8 ga watan Fabarairu – wadda ta maye gurbin tanadin ta watan Oktoban 2024, ta ayyana buƙatar hukumomin ƙasar ta hanzarta sake tsara siyasar Nijar kuma ta kasance ta zo daidai da tsarin haɗakar ƙungiyoyi uku na Sahel – AES. Bayan da ya hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yulin 2023, Janar Tiani, a wannan shekara kuma a watan Satumba ya shigar da ƙasar cikin haɗakar Mali da Burkin Faso inda suka ƙirƙiri ƙungiya mai sunan Hadakar Ƙasashen Sahel – wadda ƙungiya ce da suka yi saboda barzanar da suka riƙa fuskanta daga ECOWAS kan neman mayar da ƙasashen tsarin mulkin dumukuraɗiyya bayan juyin mulki.
Batun Bazoum

Asalin hoton, Getty Images
Mohamed Bazoum, wanda aka yi wa juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli na 2023, sojoji na tsare da shi da kuma matarsa Hadiza, a fadar shugaban ƙasa bisa wau tsauraran sharuɗɗa. Lauyoyinsa na ta kira da a sake shi, amma hukumomin sojin sun ƙi. Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya kan tsare mutum ba bisa ƙa’ida ba ta yi suka kan ci gaba da tsare Bazoum. Hukumar wadda ke bayar da rahotonta ga hukumar majalisar kan haƙƙin ɗan’Adam, ta ce babban matakin da ya fi dacewa shi ne gaggauta sakin Bazouma matarsa tare da ba su damar biyansu diyya.
Da majalisar ta nemi bahasi daga gwamnatin sojin ta Nijar game da ci gaba da tsare Bazoum da matar tasa, sai suka bayyana cewa ai ya yi waya da mayaƙa da suke adawa ko maƙiya ga Nijar domin haɗa kai da wata ƙasar waje a kai wa Nijar hari. A watan Disamba na 2023, kotun ƙungiyar ECOWAS ta bayar da umarnin sakin Bazoum amma sojojin suka yi burus da kiran, kuma abin bai ma tsaya a nan ba ƙasar ta ma fice daga ƙungiyar. Mohamed Bazoum, wanda aka zaɓa a 2021, bai sauƙa daga mulki ba kuma har yanzu yana iƙirarin cewa shi ne shugaban Nijar. Wataƙila a tattauna wannan batu a ƙarƙashin kwamitin adalci ko shari’a da ‘yancin ɗan’Adam na taron ƙasa.