Rundunar sojin Najeriya ta ce gwamnatin sojin Nijar ta amince su yi aiki tare domin yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi kasashen biyu.
Babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka bayan ganawa da hukumomin sojin Nijar a ziyarar da ya kai ƙasar ranar Laraba.
A ganawar da suka yi, ɓangarorin biyu sun amince da muhimmancin ci gaba da tattaunawa da yin aiki tare wajen tunkarar ƙalubalen tsaron da ta addabe su da kuma ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.
Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin kasashen biyu, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar.
Amma babban hafsan tsaron Najeriya ya ce sun fahimci muhimmancin Nijar kuma wasu ne suka nemi su shiga tsakanin kasar da makwabciyarta Najeriya.
“Mun duba cewa duk abubuwan da suka faru, tun a shekarar da ta gabata har zuwa yau, mun ga kuma ya kamata mu ci gaba da huldar da ke tsakaninmu kafin wannan matsalar ta shigo tsakani inda wasu suka nemi su kawo muna sabani tsakaninmu.”
“Akwai waɗanda suna so su kawo muna tashin hankali, domin a wajensu tashin hankalin suke so, amma mu kuma mun san dukkaninmu daya ne ba za mu bar su ba.”
“Mun tabbatar da mu sojoji ne ba ƴan siyasa ba ne domin aikin da muke yi na tsaro ne,” in ji Janar Christopher Musa.
Me aka tattauna?
Babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa ya ce sun tattauna ne kan yadda Najeriya da Nijar za su hada kai domin su ƙara tsaron kasashen biyu.
Ya ce kowa ya sa cewa Najeriya da Nijar yan’uwa ne, kuma sun daɗe suna aikin soji da samun horo tare.
Mun san dade ba a zauna tatattauna tare ba shi y asa mujka gay a dace um zo a tattauna kuma wannan tattaunawar za ta sa um ci gaba da aiki tare
“Yanzu mun amince za mu ci gaba da aiki tare babu bambanci, domin Nijar da Najeriya ɗaya ne, ba za mu yarda wani ya yi amfani da mu ba, ya kawo tashin hankali a tsakaninmu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, Najeriya ta roƙi Nijar ta hada kai da ita har da Chadi domin tunkarar matsalolinsu.
“Kada su yarda wani ya zo ya yi masu ƙarya ya tunzura su har su yi abin da bai kamata ba,” a cewar babban hafsan tsaron na Najeriya.
Ya ce yanzu sun fahimci muhimmanci tuntuɓa da kuma muhimmancin juna.
“Mun ga cewa rashin magana na sa saɓanin na ƙara yaɗuwa, dalilin haka ya sa muka ga ya kamata mu zo mu zauna domin mu fahimtar da juna cewa babu fada tsakaninmu.
“Muna son mu ci gaba da aiki tare yadda ƙasashenmu biyu za su samu zaman lafiya”
Za mu ci gaba da shirin da muka saba yi a baya, domin lokacin da muna aiki tare mun fi samun fahimtar juna, rashin tuntubar juna mun fahimci cewa sabani na shiga tsakani,” in ji Janar Christopher Musa.
Nijar na daga cikin ƙasashe uku na yankin yammacin nahiyar Afirka waɗanda suka fice daga ƙungiyar Ecowas bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohammed Bazoum.
Ƙungiyar ta Ecowas ta yi ta ƙoƙarin ganin ta dawo da ƙasashen zuwa cikinta, sai dai har yanzu abin ya ci tura.
Bayan ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas, ƙasashen na Sahel sun kafa wata ƙungiyarsu ta yankin Sahel ta AES.
Dukkanin ƙasashen uku na fama da matsaloli na rashin tsaro, inda suke faɗa da ƴan tayar da ƙayar baya masu iƙirarin Jihadi.
Ƙasashen uku kuma dukkaninsu sun raba gari da uwar gijiyarsu Faransa inda suka rungumi Rasha da a yanzu ke ba su taimakon soji.