Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen rediyo na BBC a tashoshin FM a fadin kasar har na tsawon wata uku.
Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta zargi BBC da watsa labaran da ba haka suke ba, wadanda ke iya rage karsashin sojojin da ke yaki da masu ikirarin jihadi.
Ministan sadarwa a Nijar, Sidi Mohammed Raliou, ya zargi gidan rediyon BBC da yaɗa labarai masu cike da kura-kurai waɗanda za su iya kawo tarnaƙi wajen samar da zaman lafiya a Nijar.
A cewarsa, a kan haka ne suka ɗauki matakin dakatar da watsa shirye-shiryen BBC na tsawon wata uku a tashoshin FM da ke faɗin ƙasar.
A cikin ƴan kwanakin nan, BBC a harsunan Hausa, Faransanci da Ingilishi na bayar da rahotanni akan lamuran da suka shafi tsaro, musamman irin gumurzun da ake yi tsakanin sojoji da kuma masu iƙirarin jihadi.
Wannan matakin na nufin a yanzu masu sauraron sashen Hausa na BBC da kuma sashen Faranshi na BBC sai dai su saurari shirye-shiryen tashoshin a mita mai gajeren zango ko kuma ta shafin intanet.
Tun a shekarar 1994, BBC ta ƙulla ƙawance da wasu gidajen rediyo masu zaman kansu da ke watsa shirye-shiryenta a zagon FM.
Wannan shi ne karo na farko da wata gwamnati a ƙasar ke dakatar da watsa shirye-shiryen BBC.
Ko a farkon watan Augustan 2023, ƴan kwanaki bayan juyin mulkin da sojojin suka yi sun dakatar da watsa shirye-shiryen gidan rediyon RFI da Talabijin na France 24 na ƙasar Faransa bisa zargin neman tayar da zaune tsaye.
A wani matakin na daban, gwamnatin mulkin sojan ta ƙuduri aniyar maka gidan rediyon Faransa (RFI) kotu bisa zargin kafar da neman haddasa fitina tsakanin al’umma da “nufin haifar da kisan ƙare-dangi.”
Tun bayan komawa mulkin soji, hukumomin Nijar sun kama tare da tsare ‘yan jarida da ‘yan kungiyoyin fararen hula, wani abu da ake yi wa kallon salo ne na take ’yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin dan’adam.
Ko a wannan mako kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta bukaci hukumomin na Nijar da su gaggauta sako wani dan kungiyar fararen hula, Moussa Tchangari, wanda aka kama a cikin wannan wata na Disamba bayan komawa gida daga wata tafiya da ya yi zuwa kasar ketare.
A ranar 26 ga watan Yulin 2023 ne sojoji suka tuntsurar da gwamnatin shugaban Nijar, Mohamed Bazoum bayan wani juyin mulki da suka gudanar, inda shugaban dakaru masu tsaron fadar shugaban ƙasar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban mulkin soji na ƙasar.
Daga baya Nijar da ƙasashe biyu masu maƙwaftaka da ita – Mali da Burkina Faso – sun haɗa kai tare da samar da ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel (AES) tare da bayyana ficewar su daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas/Cedeao.
Haka nan Jamhuriyar ta Nijar ta katse hulɗar dangantaka tsakaninta da uwar gijiyarta Faransa, da kuma dakatar da yarjejeniyar soji da ke tsakaninta da ƙasar Amurka.
Tun bayan juyin mulkin, Nijar ta fuskanci ƙarin hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke addabar yankin na Sahel.