Asalin hoton, ORTN
Yayin da za a fara babban taron ƙasa a Jamhuriyar Nijar domin tsara yadda za a mayar da mulki ga gwamnatin farar hula, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, wanda ya kifar da zababbiyar gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum, kungiyoyin fararen hula sun kauracewa halartar taron.
Ana jin cewa taron ba zai yi armashin da aka yi zato ba saboda yadda ƙungiyoyin fararen hula suka bayyana aniyarsu ta ƙauracewa taron.
Shugaban mulkin soja na ƙasar, janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya kira taron, ya ce za a yi amfani da abin da aka tattauna wajen tsara abubuwan da gwamnati zata tattauna akai da kuma lokacin mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Hakan na nuni da cewa a yayin taron za a samar da daftarin da zai yi tanadin matakan mayar da mulki ga farar hula a Jamhuriyar ta Nijar.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana yadda suke ganin taron zai kasance.
Dr Abba Sadik, mai sharhi kan harkokin siyasa da tsaro a yankin Sahel, ya shaida wa BBC cewa suna kyautata zaton a yayin taron za a samar da takarda da za a tsara yadda za a gudanar da mulkin rikon kwarya da kuma yadda za a gudanar da zabe.
To sai dai kuma rashin halartar kungiyoyin fararen hula a babban taron a Nijar ba karamin babbar illa ce ga tasirin taron ba, a cewar masana siyasa a ƙasar.
Dr Abba Sadik ya ce duk abin da ya kamata a tsara ko tattaunawa kafin taron ba a yi shi ba.
Ya ce, “Wannan taron dai na kowa ne, kuma a taron ma kwata-kwata ba a gayyaci ‘yan siyasa ba, gashi kuma ana maganar za a tattauna yadda za a mika mulki ga farar hula.”
“Idan har za a yi taro a kan abin da shafi mulkin farar hula, dole ne a sanya ‘yan siyasa a ciki, don idan basu to su wa ne zasu yi gwagwarmaya a yayin zaben”.
Tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum a watan Yulin 2023, janar Tchiani ya yi alkwarin mayar da mulki ga farar hula cikin shekaru uku, amma shafe dogon lokaci ba tare da ganin an fara daukar kwararan matakai a kan mika mulkin ba ya sanya an fara nuna shakku a kan tabbatuwar hakan.
Kazalika, akwai masu sharhin da ke ganin cewa duk da kiran gudanar da babban taron na kasa da shugaban mulkin sojin na Nijar ya yi, ba lallai su mika mulki ga farar hula ba.