Hukumomi da jama’a a jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na nuna damuwa kan ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ke gudanar da harkokinta a wasu ƙananan hukumomin jihar biyar.
Mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ne ya bayyana haka a yayin gabatar da wata maƙala a lokacin da ɗaliban kwalejin horon soja (Nigeria Defence College ) da ke Abuja suka kai wa jihar ziyara a ranar Juma’a da ta gabata.
Mataimakin gwamnan ya shaida wa BBC cewa ‘yan ƙungiyar da ake wa lakabi da Lakurawa, waɗanda suke ɗauke da manyan makamai, suna yawo tare da wa’azi ga mazauna yankunan ƙananan hukumomin Tangaza da Gudu da Illela da Binji da kuma Silame.
Daga ina Lakurawa suka ɓullo?
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ‘yan ƙungiyar sun shiga yankunan na Sokoto ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.
Sukan yi wa’azi tare da aiwa jama’a cewa su ba su tare da ‘yansanda da sojoji, da ma duk wani jami’in gwamnati na siyasa kuma ba su yarda da karatun boko ba.
Majiyar ta ƙara da cewa mutanen waɗanda suke ɗauke da manyan makamai, sukan yi wa mutane jawabi cikin harsuna daban-daban.
Bayanai sun nuna cewa idan mutanen suka yi wa’azi ko faɗakarwa sukan fassara da Hausa, da Fulatanci, da Abzinanci, da Tubanci, da Barbarci, har ma da Ingilishi.
‘’Suna da yawa sosai, idan suka zo gari da mashin 10 ko 15, sai su ajiye mutanensu a nan su ƙara gaba zuwa wani garin,’’ in ji majiyar.
Haka kuma bayanan sun nuna cewa ƙungiyar na kafa wa mazauna garuruwa dokoki, har ma suna bayar da jarin kuɗi na Sefa (CFA) ga matasa idan suka ga wanda ba shi da ƙarfin jari domin bunƙasa sana’o’insu.
Sannan kuma suna karɓar haraji da zakka. Idan ba a bayar ba sai su kwashe dabbobin mutum har sai ya biya kafin su ba shi dabbobinsa, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC.
Wani mazaunin yankin ya ce daga cikin ƙananan hukumomi biyar na wannan yanki na Sokoto, sun fi ƙarfi a biyu daga ciki wato ƙaramar hukumar Gudu – wadda ya ce in ban da hedikwatar ƙaramar hukumar babu inda mutanen ba su zuwa.
Wasu bayanai sun tabbatar wa BBC cewa ko a kwanakin baya ‘yan kungiyar sun yi arangama da jami’an tsaron Najeriya, inda suka kashe hudu, kuma su ma ‘yan ƙungiyar ya ce sun yi asarar mutanensu a lokacin.
Barazanar da Lakurawa ke yi ga Najeriya
Masana harkokin tsaro na ganin cewa ɓullar wannan ƙungiya ba ƙaramar barazana ba ce ga ƙasar idan aka yi lakari da cewa wuri ne da fitacciyar kungiya mai iƙirarin jihadi a duniya take – Ansaru – kamar yadda Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Consulting, mai bincike a kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya shaida wa BBC.
Ya ce wannan zai ƙara ta’azzara yanayin da ƙasar ke ciki na fama da matsalolin musamman yankin arewacin ƙasar ke ciki.
Lamarin ya bai wa irin waɗannan ƙungiyoyi dama ta samun gindin zama inda suke tara makamai da ƙara ƙarfi, harma suke iko a yankin, a cewar Kabiru Adamu.
“Kusan a ce babu wata hukuma ta gwamnati da ke kalubalantarsu da kyau, kasancewar yanki ne da ke da iyaka da ƙasar Mali, wadda an san irin yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke yaƙi da gwamnatocin ƙasashen.” in ji shi.
Masanin ya ce, abin zai iya kai Najeriya ga yaƙi da ƙungiyar kamar yadda take fama da wasu ire-irensu, waɗanda ke iƙirarin jihadi.
Mece ce mafita?
“Kamar yadda muka sha faɗa, tun 2014 ya kamata hukumomin Najeriya su ɗauki mataki a wannan yanki na Sokoto da ke da iyaka da Sahel, a kafa sansanin soji a wajen domin daƙile duk wata barazanar tsaro daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi,” kamar yadda Kabiru Adamu ya bayyana.
“Amma sai a baya-bayan nan suke yin hakan, inda suke ƙulla alaƙa da gwamnatocin ƙasashen yankin don fuskantar matsalar tsaron,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa irin wannan alaƙa za ta iya taimakawa sosai wajen yaƙi da matsalar ta hanyar haɗin gwiwa, inda gwamnonin jihohin yankin za su riƙa fito da tsare-tsare da za su taimaka wajen rage tasirin irin waɗannan ƙungiyoyi.
Masanin ya kuma ce akwai buƙatar a samar da tsari ingantacce na tattara bayanai da musayarsu tsakanin waɗannan jihohi na yankin, da kuma ƙasashe maƙwabta, yana mai cewa ta hakan za a iya daƙile tasirin irin waɗannan ƙungiyoyi cikin sauri.
Kabiru ya kuma ce kamata ya yi gwamnonin jihohin arewacin Najeriya har ma dai waɗanda ke irin wannan yanki da ke cikin barazanar tsaro, su kafa ma’aikatar tsaro wadda za su naɗa mutumin da ya san harkar tsaro ya shugabance ta, tare kuma da ba shi wuƙa da nama, ya ba shi abubuwan da duk ya kamata ya yi aiki.
Ya ce har yanzu abin takaici babu wani gwamna a arewacin najeriya da ya yi haka saɓanin wasu jihohin kudancin Najeriya, kamar Lagos da Edo da suka yi haka.
Masanin ya kuma ce ya kamata gwamnatin tarayya ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi wanda hakan zai ƙarfafa wa jihohin gwiwa, sannan su riƙa yin abu tare maimakon kowanne na nashi daban.
Sannan ya ce akwai buƙatar shigar da jama’a cikin harkar tsaron domin idan ba gwamnati ta ba shigar da jama’a ba, idan ba ta shawo kan jama’a ba to ta bar su ƙungiyoyin masu kirarin jihadin su ja jama’ar kenan – domin komai saboda jama’a ake yi su ƙungiyoyi jama’a suke nema.
Haka kuma ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da tsaro na gari tare da adalci ta yadda duk wani mai ƙaramin ƙarfi idan aka danne masa haƙƙinsa ya kai ƙara a ƙwato masa haƙƙi – ”ba sai mutumin da yake da kuɗi ba,” in ji masanin.