Asalin hoton, Getty Images
Mabiya addinin Kirisita a fadin duniya na gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.
Bikin na farawa daga dare na Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a, sannan a kammala a ranar Litinin ta gaba.
A tattaunawarsa da BBC, Rabaran Murtala Mati Dangora, babban malamin addinin kirista a Najeriya, ya ce bukukuwan Easter sun kasu kashi biyu; akwai Juma’a mai Tsarki (Good Friday) da kuma Easter Monday.
Rabaran Dangora ya bayyana cewa “Juma’a mai Tsarki rana ce ta saduda, ta dawo ga Allah, da rana mai tunani domin wahalar da Yesu Almasihu ya sha.”
“A ranar ne aka zartar masa da hukuncin kisa a bisa umarnin sarkin Pontius Bilatus, a ranar ne sojojin Romawa suka gicciye shi, a ranar ne ya mutu, a ranar ne kuma aka saka shi a kabari,” in ji shi.
Ya kara da cewa: “Abin da aka bayyana a cikin littafin tsohon alkawari ya auku ne a rana ta uku bayan da Romawan suka gicciye shi a wani waje da ake kira Calvary ko Golgotha a wajen birnin Kudus.”
Reverend Dangora ya ce wannan rana ba ta shagali ba ce kawai, amma rana ce da ake son duk mabiya addinin Kirista su yi biki cikin neman salama.
“Duk lokacin da ranar Juma’a mai Tsarki ta kewayo, mukan yi kira ga jama’a da su kasance cikin saduda, da komawa ga Allah, suyi tunani kan cewa rai mai mutuwa ne, domin idan har Almasihu ya mutu, ba wanda zai guje wa mutuwa.”
‘Yadda aka gicciye Yesu Almasihu
Rabaran Dangora ya kara bayani game da tarihin gicciyewar Yesu Almasihu, inda ya ce daya daga cikin almajiransa, Yahuza, ya ci amanarsa ya bayar da shi ga abokan gabansa.
“An fara wannan tun ranar Laraba zuwa Alhamis, har ya zuwa ranar Juma’a da aka zartar masa da hukunci, kamar yadda Romawa ke yi wa wadanda suka aikata laifi,” a cewarsa.
Ya kara da cewa “kodayake Yesu Almasihu ba ya aikata laifi ba, ya dauki zunubanmu ne, ya sa aka kama shi a matsayin mai laifi.”
Malamin na Kirista ya ce gicciyewar da aka yi masa ya shafe sa’oi uku zuwa hudu kafin a bayyana cewa ya mutu. Daga nan, wani almajiri da ake kira Yusuf ya roki alfarma daga sarki don ya samu gangar jikin Yesu Almasihu don yi masa jana’iza.
“Yadda Yahudawa suke jana’iza ya bambanta da yadda muke yi, yayin da muke rami mu jefa mutum, su kuma suna tanadi rami ga duk wanda ya rasu. Yesu Almasihu ya riga ya tanadi wannan rami da aka rufe da hatimin hukuma.”
Rabaran Dangora ya ce saboda farkon kafa addinin Kirista ne, dalilin da ya sa mabiya addinin suka shiga damuwa. Lokacin da aka zo za a kama Yesu Almasihu, daya daga cikin almajiransa, Bitrus, ya zaro takobi ya sare wani har ya cire masa kunne.
A cewarsa: “Yesu Almasihu ya ce masa, a’a Bitrus, idan ina so zan iya umartar mala’iku su je su hallaka su, amma yaki ba na nama da jini ba ne, don haka ka mayar da takobinka, domin wannan ya zama cikar annabci.”
Rabaran Dangora ya nuna yadda mabiyan ke muhimmantar da wannan rana wajen yanka rago da zubar da jini wanda ke misalta Yesu don tunawa da ‘yanci daga zunubi.
Ya ce mabiyan kan bayar da kyaututtuka lokacin bikin Easter, yana kira ga mabiya addinin Kirista da su koma ga Allah, suyi azumi, neman tuba da kiyaye hanyar da Yesu Almasihu ya bar musu.