Asalin hoton, Reuters
Wata kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari ko kuma su biya tarar dala 7,700 saboda yunƙurin fasa-ƙwaurin dubban sarauniyar tururuwa daga ƙasar.
An kama waɗanda ake zargin su huɗu ne – biyu ‘yan Belgium da ɗan ƙasar Vietnam sai kuma wani ɗan Kenya – cikin watan jiya da dubban tururuwa mai rai kuma ana zargin za su kai su ƙasashen Turai da na Asiya.
Sun dai amsa tuhume-tuhumen da aka yi musu, har ma ‘yan ƙasar Belgium ɗin suka faɗa wa kotun cewa sun kama tururuwar ce wadda ake matuƙar nema saboda nishaɗi, kuma ba su san yin hakan laifi ba ne.
Sai dai a hukuncin da ta yanke ranar Larabar nan, alƙalin ta ce nau’in tururuwar da suka kama na da matuƙar daraja kuma sun kwashi dubbai, ba ma ‘yan kaɗan ba.
Majistare Njeri Thuku ta ce ana iya ɗaukar kama tururuwa ‘yan kaɗan a matsayin nishaɗi, amma ba kama sarauniyar tururuwa har 5,000 ba.
“Tuni duniya ta yi asarar nau’o’in tururuwa a wani ɓangare saboda haɗama. Don haka lokaci ya yi da za a dakatar da wannan al’amari.
Daga cikin nau’o’in tururuwar har da wata wadda da Ingilishi ake kira African harvester ant, kuma wasu dillalai a Birtaniya na sayen duk ƙwaya ɗaya a kan fam 170.