Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya baiwa masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari da aka saki kyautar Naira dubu 100 da wayoyin hannu kowannesu.

Gwamna ya kuma yi alkawarin sake tsugunar da masu zanga-zangar da suka fito daga Kaduna da aka saki su 39 tare da tallafa musu matukar suka canza hali.

Sakataren gwamnatin jihar Kaduna Abdulkadir Mayere wanda yayi jawabi a madadin Gwamna Uba Sani ya bayyana cewar gwamnan ya umarce shi ya karbi takardun karatun wadanda suka kammala makarantun gaba da sakandare daga cikinsu.

Haka kuma sakataren gwamnatin ya kara da cewar gwamnatin jihar Kaduna zata cigaba da bibiyar ayyuka da dabi’un masu zanga-zangar da aka saki su 39 domin tabbatar da cewa sun zamo nagartattun mutane kafin ta cika musu alkawuran data daukar musu.

A cewarsa, an gudanar da gwajin lafiya ga masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagarin da aka sako din tare da basu shawarwari akan yadda zasu zamo mutane nagari da zasu amfani kansu dama al’umma baki daya.

Zanga-zangar ta gudana ne a watan Agustan da ya gabata sakamakon mummunan matsin tattalin arziki a Najeriya.

A akasarin wurare zanga-zangar ta kasance ta lumana sai dai daga bisani ta rikide zuwa tarzoma a wasu sassa na kasar da ta janyo barnata dukiya.

Watanni bayan zanga-zangar, gwamnatin tarayyar Najeriya ta gurfanar da wasu daga cikin masu zanga-zangar a bisa tuhume-tuhume 10.

Sai dai hakan ya janyo fushin al’umma bayan data bayyana cewar wasu daga cikinsu yara ne kankana.

Hakan ta janyo Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bada umarnin sakinsu.

By Ibrahim