Shaidun gani da ido da dama sun tabbatar da cewa, Kamfanin NNPCL ya rage Naira 20 kan kowacce litar mai a sassa daban-daban na birnin tarayya Abuja.
Bayanin Ibrahim Isa, wani mai abin hawa da Muryar Amurka ta yi hira da shi ya tabbatar da cewa, gidajen man NNPCL na aiwatar da sabon farashin da aka rage, labarin da ya yi ta yaduwa a kafoffin yada labalai na yanar gizo.
A nashi bayanin, Aliyu Muhammad Tukur, ma’aikaci a gidan man Azman ya shaida wa Muryar Amurka cewa, suna rage nasu farashin ne sakamakon yanayin rashin samun kasuwa.
Sai dai wasu ‘yan kasar sun ce matakin rage farashin litar mai da kamfanin NNPCL ya dauka ya nuna rashin tausayin talakawa ne kawai ganin irin gagarumin sauyin da aka gani a kasa da shekaru biyu a farashin kowacce litar mai a Najeriya.
Wani jigo a a kungiyar IPMAN Dakta Zarma Mustapha ya ce rangwame da aka samu a kudin sauke kaya na daga cikin dalilan da ya kawo ci gaban da aka samu, ya na mai tabbatar da cewa, ba gidajen man NNPC kawai suka rage farashi ba, har ma da mambobin kungiyar su ta IPMAN wanda nasu ragin ke tsakanin Naira 20 zuwa 40.
Dangane da bambanci tsakanin farashin dauko mai daga matatar man Dangote da na NNPCL, Dakta Zarma Mustapha ya ce suna dauko kaya daga matatar Dangote a kan Naira 970 kowacce lita a bisa sharadin sayen lita miliyan biyu.
Wasu majiyoyi masu karfi da suka bukaci a sakaya sunan su sun ce man kamfanin NNPCL ya fi na matatar Dangote tsada.
Sauye-sauye a farashin litar man fetur a cikin kasa da shekaru biyu a Najeriya na ci gaba da jefa talakawa cikin matsi sakamakon wasu abubuwa da suka hada da cire tallafi, matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka a ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki, lamarin da masana tattalin arziki suka ce ya jefa ‘yan kasar cikin wani rin munin tsadar rayuwa.