Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana cewa kasafin kudin kasar na 2025 ya yi hasashen raguwar hauhawar farashin kaya daga kaso 34.6% da take a yanzu zuwa kaso 15% a shekara mai kamawa.
Ya gabatar da wannan hasashen ne a lokacin da yake bayyana kasafin kudin Najeriya na 2025 wanda ya kai Naira tiriliyan 47.9 gaban majalisu biyu a yau Laraba.
Shugaban ya kuma bayyana cewa harkar canjin dalar Amurka za ta inganta daga kimanin Naira 1,700 zuwa Naira 1,500.
“Kasafin ya yi hasashen cewa hauhawar farashi za ta sauka daga kaso 34.6% zuwa kaso 15% a shekara mai kamawa, yayin da musayar kudin dalar Amurka za ta inganta daga Naira 1,700 zuwa Naira 1,500. Ana zaton kuma yawan danyen man da Najeriya za ta rika hakowa a kowace rana zai kai tsakanin ganga miliyan 2 zuwa miliyan 2 da rabi,” in ji Tinubu.
Ya kara da cewa wannan hasashen an dora shi ne bisa mizanin lura da abubuwa kamar raguwar albarkatun man fetur din da Najeriya ke shigowa da su daga ketare, da kuma kara yawan fitar da tatattun albarkatun man, tare da samun kaka mai kyau sakamakon inganta yanayin tsaro da rage dogaro akan shigo da kayan abinci.
‘Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki sakamakon yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi, tare da rashin tabbas a kasuwar musayar kudade da ya sanya canjin dalar Amurka ya kai Naira 1,700 a baya-bayan nan.
Jumlar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta karu zuwa kaso 34.60% a watan Oktoban 2024, bisa ga rahoton hukumar kididdigar kasar (NBS) da aka fitar a yau Litinin.
Hauhawar farashin ta watan Nuwamba ta bayyana karin maki 0.72% idan aka kwatanta da na watan Oktoban 2024, bisa ga rahoton alkaluman auna farashin kayayyakin masarufi (CPI) na NBS na baya-bayan nan.