Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da dokar matsakaicin kasafin kudi da ta dabarun sarrafa kudi domin aiwatarwar gwamnatin tarayyar kasar.

Zartar da dokar ya biyo bayan gabatar da rahoton da shugaban kwamitocin hadin gwiwa na kudi da tsare-tsare da al’amuran tattalin arziki, Sanata Musa Muhammad Sani (mai wakiltar Neja ta gabas) ya yi.

Haka kuma Majalisar Dattawan ta dora wa kwamitocinta a kan kudi da albarkatun man fetur da iskar gas alhakin bincikar zarge-zargen rike kudade da kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya yi, ciki har da Naira tiriliyan 8.48 na tallafin man fetur, da dala biliyan 2 (kwatankwacin naira tiriliyan 3.6) na kudaden harajin da ba a biya ba.

Rahotannin hukumomin NEITI, mai fafutukar tabbatar da adalci a harkar hakar ma’adinai data rabon arzikin kasa (RMAFRC) suka fayyace zarge-zargen.

Hakan na zuwa ne sakamakon sanarwar da ofishin babban mai binciken kudi na tarayya ya yi, na cewa ta samu dukkanin takardun da ta bukata domin tantance bukatar biyan Naira tiriliyan 2.7 ta kudaden tallafin man fetur din da NNPCL ya gabatar wa gwamnati.

Majalisar ta amince da hasashen yin musayar dalar Amurka a kan naira 1, 400 dake cikin karamin kasafin kudin 2025 zuwa 2027 da damar sake nazarin hakan a farkon shekarar 2025, a bisa la’akari da manufofin kudin da ake aiki dasu.

By Ibrahim