Ana gudanar da bikin Kirsimeti a ranar 25 ga watan Disambar kowacce shekara, inda mabiya addinin Kirista ke tunawa da haihuwar Isa Almasihu.
Bikin na Kirsimeti a wannan shekara ya sha banban da sauran shekarun da suka gabata, saboda yadda al’ummar Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki, wanda ke shafar rayuwar al’umma ta yau da kullum.
‘Ƴan Najeriya dake shirin gudanar da bikin Kirsimeti sun shaida wa Muryar Amurka cewa, matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar ya tasiri kan shirye-shiryen bikin na bana.
A hirarsa da Muryar Amurka, Pastor Joshua Maikudi Matazu, ya ce duk da wannan hali, kamata yayi al’ummar Kirista su mayar da hankali wajen ibada a wannan rana, tiyin ba wai shagulgula ko kashe kudade ba tare da lissafi.
Pasto Matazu ya kara da cewa, al’ummar Kirista su dukufa da ibada kamar yadda addinin Kirista ya koyar, ta haka za a kawo karshen halin kunci da ake fama da shi a kasar.
A daya bangaren, hauhawar farashin sufurin mota a kasar ya jefa ‘yan kasa cikin wani yanayi, musamman a lokacin shirye-shiryen bikin Kirsimeti. Bulama Kaku Ali, shugaban kungiyar NURTW reshen Jihar Yobe, ya shaida cewa, hauhawar farashin litar man fetur da bukatun motoci kafin sufuri na daga cikin dalilan da ke haifar da hauhawar farashin sufurin.
Yanzu dai abin jira gani shine yadda saukar farashin litar man fetur zai yi tasiri wajen saukaka lamura a kasar.