Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana aniyarta ta yin amfani da fasahar kirkirarriyar basira wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ministan Harkokin Sadarwa da Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Dr. Bosun Tijani, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja a jiya Alhamis.

Google

Google

Ya kara da cewar gwamnatin Najeriya ta samo tallafin naira Biliyan 2.8 daga, kamfanin fasahar sadarwa na Google da nufin bunkasa fasahar kirkirarriyar basira a kasar.

Tijani ya ci gaba da cewa, gwamnatin za ta maida hankali a fannoni irinsu lafiya da noma da ilmi da harkar mulki wajen shawo kan matsalolin cikin gida da tabbatar da dorewar bunkasar tattalin arziki ta hanyar kirkirarriyar fasaha.

A nasa bangaren, Matt Brittin, Shugaban Kamfanin Google EMEA, yace za’a aiwatar da tallafin a Najeriya ne ta hanyar shirin gwamnatin na samar da fasahohin kirkire-kirkire milyian 3 (3MTT) da zai maida hankali wajen samar da ‘yan Najeriya 20, 000 dake da fasahar kirkirarriyar basira.

Manufar shirin 3MTT, da aka kaddamar a ranar 13 ga watan Oktoban da ya gabata, da za’a shafe shekaru 4 ana gudanarwa shi ne baiwa ‘yan Najeriya horo da gina kashin bayan fasahar kirkire-kirkiren kasar tare da mayar da Najeriya kasar da za ta rika kasuwancin fasaha zuwa ketare.

Brittin ya ci gaba da cewa ta hanyar shirin, za’a baiwa malamai 125, 000 horo sannan za’a tallafawa kananan kamfanoni 10 da suka nuna kwazo a harkar kirkirarriyar basira da Naira miliyan 100.

By Ibrahim