Sai dai masana tattalin arziki na ganin yawaitar karbar rancen kudade da gwamnatin kasar ke yi, ka iya jefa tattalin arzikin kasar cikin wani karin mawuyacin hali.

Ministan Kasafin Kudi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ne ya bayyana hakan, a lokacin da tawagar Asusun Lamuni na Duniya, IMF suka kai masa ziyara karkashin jagorancin babban wakilin asusun a Najeriya, Mr. Axel Schimmelpfennig.

Atiku Bagudu, ya ce, “rancen dala miliyan 500, da suke shirin karba, zai mayar da hankali ne wajen bunkasa harkar ilimi a matakin farko da inganta harkar lafiya a jihohin kasar, samar da ayyukan yi da kuma inganta tsarin koyarwar malamai.

Bagudu, ya kara da cewa “gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, na kokarin farfaɗo da tattalin arzikin kasar, da kuma na haraji, ta yadda kasar za ta kasance me dogara da kai wajen samun kudin shiga”.

Kazalika, Ministan, ya ce ‘“ƴan kasar na cikin mawuyacin hali, biyo bayan cire tallafin man fetur, rashin tabbas a kasuwar musayar kudade da kuma sabon tsarin wutar lantarki, wanda an yi su ne domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar”.

A hirarsa da Muryar Amurka, Dr. Mainasara Nasiru, masanin tattalin arziki a jami’ar Usman ‘Dan Fodiyo dake Sokoto, ya ce “karɓar rance da gwamnatin kasar ke yi, barazana ce ga tattalin arzikin kasar, idan har ba a aiwatar da ayyukan da suka dace da kuɗaɗen ba”.

Dr. Nasiru ya kara da cewa “kaurin suna da Najeriya tayi wajen cin hanci da rashawa, idan kuma aka yi la’akari da kuɗaɗen da ake rantowa, maimakon a aiwatar da ayyukan da suka dace, karshe kuɗaɗen sulalewa suke a aljihun wasu tsiraru, wanda hakan yasa ke shafar ingancin tattalin arzikin kasar”.

Hassan Sardauna, dake sharhi kan lamurran da suka shafi kasa da siyasa, na ganin yawan karbar rance da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke yi, abin tashin hankali ne.

Hassan Sardauna ya ce “a shekarar 2024 kadai, Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta karbi rance da da ya zarta Triliyan 100, kuma ya dace ace ƴan kasa na ganin ayyukan da ake yi a kasa, ba wai kuɗaɗen su bace a sharholiya ba”.

Ƴan kasar dai na bayyana damuwarsu game da irin basussuka da ake bin kasar da ya haura Naira triliyan 134.

Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:

By Ibrahim