Abuja —
A wannan shiri, za a ji manyan baki: Masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu, dan Majalisar Wakilai Abubakar Yahaya Kusada, da Alhaji Musa Abubakar Dan Malikin Kebbi. Suna bayani kan dalilan da ya sa Najeriya ba za ta iya rayuwa ba tare da cin bashi har zuwa wani lokaci nan gaba, duk da cewa wani daga cikin su ya bayyana takaicinsa kan haka. A yi sauraro lafiya.