A yau Talata Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’ar kasar ta yi aiki da majalisar dokoki domin gyara ababen da ke janyo ce-ce-ku-ce a kudirin gyara dokar haraji.
“Shugaba Tinubu na maraba da duk wani gyara da zai sauya duk wata saɗara da ke jawo cecekuce a ƙudirin,” a cewar Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris cikin wata sanarwa da ya fitar.
Shugaba Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin Najeriya da kudurorin ne makonnin da suka gabata.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi zargin cewa jihohin Legas da Ribas ne kawai za su iya samun gajiya daga sauya dokar harajin
Gwamnan wanda ya kasance bako a cikin shirin siyasar tashar talabijin ta Channels na ranar Lahadi da ta gabata yace bincike da kididdigar da gwamnonin arewa suka gudanar ne ya gano hakan.
To sai dai kwararre a fanin tattalin arziki Shuaibu Idris Mikati, na cewa a ka’ida na dan adam ya kamata a rika sauya dokoki ko a yi wa hukunce-hukunce kwaskwarima, domin a samu gudanarwa cikin sauki.
Mikati ya ce tun ba yau ba ake sauye-sauye kan haraji a kasar, kuma har sunan hukumar karban harajin ma an gyara mata fuska, inda ya kara da cewa yin irin wannan gyara zai taimaka wajen saita kasar.
Amma shugaban kungiyar CISLAC Auwal Musa Rafsanjani, ya yi bayanin cewa in har tsarin dimokradiyya ake bi, kuma ana yin doka ne domin jama’a, ya kamata shugaban kasa ya janye dokar har sai an shirya.
Rafsanjani ya ce gwamnonin jihohin kasar da masu fada a ji sun nuna cewa lokaci bai yi ba da za a kawo wannan doka da ta shafi sauya fasalin haraji.