Asalin hoton, X/DEFENCE HQ

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama gawurtaccen ɗanbindigar nan mai suna Abubakar Bawa Ibrahim da aka fi sani da suna Habu Dogo.

Cikin wata sanarwa da rundunar ke fitarwa a kowane mako, mai ɗauke da sa hannun, daraktan yaɗa labaran hedikwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce an kama Habu Dogo ne a ƙauyen Rumji da ke yankin ƙaramar hukumar Illela a jihar Sokoto.

Ɗanbindigar ya kasance cikin jerin sunayen da sojojin Najeriya da Nijar ke nema ruwa a jallo, saboda yadda yake addabar yankunan ƙasashen biyu, ta hanyar kai musu hare-hare, da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa dakarunta da ke aiki a kudu maso gabashin ƙasar sun kama wasu manyan kwamandojin IPOB guda bakwai a yankin.

Sojojin sun ce sun kama manyan kwamandojin ƙungiyar a jihohin Anambra da Imo da Abia.

”A tsawon kwana bakwai dakarunmu sun samu nasarar kashe ‘yanbindiga 187 tare da kama 262, da kama ɓarayin mai 39, tare da kuɓutar da mutum 147 da aka yi garkuwa da su”, in ji sanarwar.

Sojojin sun kuma ce sun samu nasarar daƙile yunƙurin satar mai a yankin kudu maso kudancin ƙasar ta aka ƙiyasta kuɗinsa da naira biliyan 1.5.

”Mun kuma ƙwato makamai 205 da harsasai 5,241”, kamar yadda Manjo Janar Buba ya bayyana.

By Ibrahim