Babbar ɓaraka ta kunno kai a tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta jam’iyyar NNPP, yayin da ‘yan majalisar tarayya biyu a jihar suka sanar da ficewa daga tafiyar.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, Ali Sani Madakin Gini ya tabbatarwa da BBC cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsa ta NNPP.

Ɗan majalisar mai wakiltar Dala a tsakiyar birnin Kano ya tabbatar da haka ne bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda a ciki aka ji yana cewa “Daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya”.

A cikin bidiyon Ali Madakin Gini ya bayyana cewa “Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce”.

Ya ƙara tabbatarwa da BBC cewa: “Na fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso”.

Haka shi ma takwaransa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da kuma Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da raba gari da tafiyar ta kwankwasiyya.

A zantawarsa da BBC, Hon. Rurum ya ce ya fice daga tafiyar ne sakamakon ”rashin adalci” daga ɓangaren uban tafiyar, Rabi’u Kwankwaso.

Zuwa yanzu dai ba a ji wani martani daga ɓangaren Sanata Kwankwaso ba a kan wannan ikirari.

Duka ‘yan majalisar biyu sun bayyana cewa har yanzu sunan nan a jam’iyyarsu ta NNPP, amma ba tsagin jagorancin Sanata Rabi’u Kwankwaso ba.

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano, wanda jam’iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.

‘Yan majalisun biyu – Ali Madakin Gini, da Kabiru Alhassan Rurum – sun yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da cewa shi mutumin kirki don haka suka shawarce shi da ya yi duk yadda zai yi, ya ”tsaya da ƙafarsa”.

A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai taken ‘Abba Tsaya da Ƙafarka’ mai rajin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa, lamarin da ya janyo jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina, bisa zarginsu da alaƙa da ƙungiyar.

By Ibrahim