Yayin da wasannin kwallon ƙafa da na kwando da zari-ruga suka yi fice a duniya, akwai kuma wasu nau’ikan wasannin gargajiya da ke bayyana al’adun wasu ƙabilu.

Ɗaya daga cikin su shi ne wasan Langa, wani nau’in wasan gargajiya da ake gwada ƙarfi wanda ya samo asali daga arewacin Najeriya.

Langa wasa ne da ke nuna juriya, ƙwazo, da tunani mai zurfi. “Al’ummar Hausawa na yi wa langa kallon wasan masu ƙarfi da jarumai,” inji Khalid Hussein, shugaban ƙungiyar masu wasan Langa ta jihar Kano.

By Ibrahim