Hukumar ƙididdiga ta ƙasa a Najeriya ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma 24.48 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.
Wannan ne karon farko da National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma, wanda ke nufin cewa a yanzu yana da wuya a tantance haƙiƙanin raguwa ko hauhawa.
Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 bisa ga tara tare da shekara ta gabata.
Kafofin yaɗa labarai na Najeriya sun ruwaito shugaan hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, na faɗa a ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne don “daidaita shi da na sauran ƙasashen duniya.”
Ya bayyana cewa karo na ƙarshe da Najeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ya kasance a shekarar 2009, inda aka ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan lokacin.
Hakan na nufin yanzu za a dinga kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka dinga amfani da ita a baya.
“A sabon tsarin, ba kawai mun matso da alƙaluman kusa da halin da ake ciki ba, mun kuma ƙaddamar da sabuwar hanyar tattara bayanai don inganta yadda muke adana su da kuma sahihancinsu,” in ji shi.