Asalin hoton, Tinubu/Facebook
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kammala shirye-shiryen gaggawa domin kwashe ƴan ƙasarta da suka maƙale a ƙasashen Isra’ila da Iran, bayan rikicin da ya tsananta tsakanin ƙasashen biyu.
A wata sanarwa da aka fitar a daren Talata, Kimiebi Ebienfa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, ya bayyana cewa jakadun Najeriya a Tel Aviv da Tehran suna ci gaba da tuntuɓar ƴan ƙasar da rikicin ya rutsa da su, domin tabbatar da cewa an kwashe su cikin aminci.
Ma’aikatar ta buƙaci ƴan Najeriya da ke zaune a Isra’ila da Iran su bi dukkan matakan tsaro da hukumomin ƙasashen suka shimfiɗa, tare da hanzarta tuntuɓar ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa don yin rajista da samun ƙarin shawarwari.
Hakanan, ma’aikatar ta yaba wa jajircewar ofisoshin jakadancin Najeriya a Isra’ila da Iran wajen tuntuɓar ƴan ƙasar a wannan lokaci mai wahala, tare da jaddada cewa kariyar lafiyar ƴan Najeriya a kasashen waje na daga cikin abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci.
“Ma’aikatar harkokin waje na sanar da cewa sakamakon rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin tarayya na kammala shirye-shiryen kwashe ƴan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen biyu.” in ji sanarwar.
Sanarwar ta biyo bayan hare-haren sama da Isra’ila ta kai a ranar Juma’a, inda ta hari wurare masu yawa a Iran, tare da kashe manyan jami’an sojin Iran da dama.