Asalin hoton, AFP

Gwamnati soja ta Janar Tchiani a Nijar na cigaba da shan suka kan wata doka da ta kafa da ke kwace izinin ɗan kasa ga duk wani mutum da aka samu da zargin laifukan ayyukan ta’addanci ko cin amanar kasa.

Tun lokacin da aka sanar da kuma soma aiwatar da dokar ake samun kungiyoyi da ‘yan adawa da ɗaiɗaikun jama’a da ke fitowa su na alla-wadai da wannan tsari.

Dokar wadda tuni ta soma aiki ta kasance abin da ake tafka muhawara a kanta inda a wannan lokaci ma kungiyoyin kare hakkin bil Adama da masana da kwararru suka shirya wata babbar mahawara kan batun dokar.

Mahawarar da masana ilimin dokoki da lauyoyi da ‘yan fafutukar kare hakin dan Adam suka nazarta na nuna wannan tsari ba abu ne da za a zura ido gwamnati na yin yadda ta ga dama ba, abin da yasa a karon farko suka fito suna wannan zama.

By Ibrahim